An sake zaɓar Mai’adua a matsayin shugaban NULGE na Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi ta ƙasa (NULGE) reshen jihar Katsina ta sake zaɓen Nasiru Wada Mai’adua a matsayin shugabanta tare da wasu mutane 12 a karo na biyu da za su cigaba da jagorantar ƙungiyar nan da shekara 3.

Zaɓen da ya gudana a hedikwatar ƙungiyar da ke Katsina an bi ta hanyar sasantawa a tsakanin ƴan takara kamar yadda tsarin mulkin ƙungiyar ya tanada.

A jawabinsa bayan bayan kammala zaɓen gwamna Dikko Raɗɗa wanda ya sami wakilci na sakataren gwamnatin jihar Abdullahi Garba Faskari ya tabbatar da gwamnati zata Cigaba da aiki tare da kungiyar domin cigaban karkara.

Gwamnan ya kuma jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ba kananan hukumomi a jihar cikakken yancin cin gashin kansu tare da yaba wa ƙananan hukumomi bisa irin haɗin kai da suke bai wa gwamnatin jihar wajan aiwatar da manufofinta.

Da ya ke jawabi shugaban ƙungiyar Nasiru Wada ya bayyana wasu nasarorin da ƙungiyar ta samu a tsawon mulkin.

“Nasarorin kuwa sun haɗa da tabbatar da ƴaƴan kungiyar sun kai matakin albashi na 16 da kuma tabbatar da ana biyan ma’aikatan albashi akan lokaci.”

Shugaban ƙungiyar ya sanar da cewa nan bada jimawa ba ƙungiyar za ta buɗe shagon sayen kayan masarufi a ƙananan hukumomin 34 da ke jihar domin sauƙaƙa wa ƴaƴan kungiyar halin matsin rayuwa.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin Katsina da ta sa ƴan kungiyar wajen rabon kayan aikin noma.

Shugaban ƙungiyar ƙwadago a jihar, Hussaini ‘Yanduna a nasa jawabin, ya yaba wa gwamntin Dikko Raɗɗa da ta fara biyan sabon tsarin albashi.

By Babaji