Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Dakarun Brigade 1 na rundunar haɗin guiwa ta Operation Fansan Yamma tare da haɗin gwiwar jami’an tsaron farin kaya ta jihar sun cafke wata mota ɗauke da tarin makamai a ƙaramar hukumar Ƙaura Namoda ta Jihar Zamfara.
Jami’in hulɗa danjama’a kan yaɗa labarai na rundunar Operation Fansan Yamma, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Gusau yau Talata.
Yace samamen da aka gudanar a ranar 27 ga watan Janairun 2025, ya samo asali ne daga bayanan sirri game da wasu da ake zargin dilolin makamai da suka shigo daga Jamhuriyar Nijar a jihar.
“Sojojin sun ƙaddamar da wani samame a ɓoye domin zaƙulo waɗanda ake zargin, lamarin da ya sa suka bi hanyar Ƙaura Namoda zuwa Zurmi”. Yace
A cewar sanarwar, waɗanda ake zargin sun yi yunƙurin tserewa ne ta hanyar karkata da motar da suke ciki cikin daji amma sai suka yi watsi da ita bayan da sojojin suka kewaye ta da su.
“Binciken da aka yi na motar ya kai ga kwato bindigogin PKT guda 2x, bindigogin AK-47 x 9, Magazine 13x, harsashi na musamman 171 x 7.62mm, da harsashi 9x na PKT”. Sanarwar ta ci gaba da cewa.
Laftanar Kanar Abubakar ya ci gaba da cewa, sojojin na ci gaba da neman riƙaƙƙen ɗan ta’addan nan Bello Turji ruwa a jallo, wanda ke ci gaba da tserewa daga maɓoya zuwa maɓoya.
“Muna tabbatar wa jama’a cewa sojojin mu suna bakin ƙoƙarin su wajen kama shi Bello Turji a wani ɓangare na kokarin mu na tabbatar da tsaron al’ummar mu”.
Sojojin sun yaba da goyon bayan jama’a game da lamarin matsalar tsaro, Hakazalika sun buƙaci jama’ar yankin da su ci gaba da bayar da haɗin kai ta hanyar bayar da rahoton duk wani bayani da zai taimaka don yaƙar ‘yan’taadda a jihar.
