Shettima ya ƙaddamar da taron MSME Clinic na shida

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Mataimakin shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ƙaddamar da taron MSME Clinic na shida tare da sanar da bayar da tallafin N300,000 ga kowanne mai sana’a da ya halarci taron a Jihar Borno. Taron da aka gudanar a fadar gwamnatin Jihar Borno a Maiduguri yana da nufin ƙarfafa ƙanana da matsakaitan ‘yan kasuwa don bunƙasa tattalin arzikin yankin.

Shettima ya bayyana cewa wannan tallafi na musamman daga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba rance ba ne, kuma yana da nufin tabbatar da ɗorewar harkokin kasuwanci a jihar. Ya kuma ƙara da cewa, cibiyar Fashion Hub da aka ƙaddamar a Borno za ta iya samar da ayyuka har 48,000 a shekara, wanda hakan zai ƙarfafa ɓangaren masana’antar ɗinki da kayan sawa a jihar.

Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yaba da wannan shiri, yana mai cewa gwamnati ta ƙuduri aniyar tallafawa ƙananan ‘yan kasuwa domin farfaɗo da tattalin arzikin jihar da rage tasirin matsalolin tsaro da rikice-rikicen da suka shafi kasuwanci. Ya bayyana cewa gwamnatinsa tana gudanar da shirye-shirye da suka haɗa da bayar da rancen jari, gina kasuwanni na zamani, da gyaran cibiyoyin koyon sana’o’i don karfafawa ‘yan kasuwa.

Gwamna Zulum ya ƙara da cewa taron MSME Clinic zai mayar da hankali kan ɓangarori guda biyar: bayar da kuɗaɗe, koyar da sabbin fasahohi, samar da kayayyakin more rayuwa, haɓaka kasuwanci, da amfani da fasahar zamani. Ya buƙaci ‘yan kasuwa su ci moriyar wannan dama don bunƙasa sana’o’insu da faɗaɗa kasuwancinsu.

A yayin taron, Shettima ya kuma ƙaddamar da Borno Fashion Hub a tsohuwar makarantar Kashim Ibrahim College of Education tare da buɗe reshen haɗin gwiwar WEMA Bank. Cikin manyan baki da suka halarta akwai ministan noma da tsaron abinci, Sanata Abubakar Kyari, ministan masana’antu na Jiha, Sanata John Owan Enoh, da dai sauran manyan mutane

By ukarofi