Dala Biliyan 29: Mata za su jagoranci farfaɗo da Afrika – Shettima

Spread the love

Ya ƙaddamar da shirin #SheIsIncluded don cike giɓin jinsi a fannin kuɗi da tattali

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A wani mataki na inganta daidaito tsakanin jinsi da ƙarfafa tattalin arzikin mata, Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya bayyana cewa, mata za su kasance a sahun gaba wajen sauye-sauyen bunƙasa tattalin arzikin Afirka da aka yi hasashen za a kashe Dalar Amurka tiriliyan 29.

Ya bayyana ƙwaƙƙwaran yaƙinin cewa, haɗa jinsi ba wai alfarma ba ce kawai, amma ginshiƙi ne na ajandar ci gaban Nijeriya.

Sanata Shettima ya bayyana hakan ne jiya Alhamis a Abuja lokacin da ya buɗe taron yaƙi da bambancin jinsi na shekarar 2025 tare da ƙaddamar da shiri mai laƙanin #SheIsIncluded, don cike giɓin da ke tsakanin jinsi a fannin kuɗi da tattalin arziki.

Taron mai taken ‘Sake shingaye, Gina Juriya don ɗorewar Mata A Tattalin Arziki da Kuɗi,’ an gina shi ne a kan ‘2024 Aso Accord for Economic and Financial Incorporated’ da kuma jaddada aniyar Nijeriya na cimma burin ci gaba mai ɗorewa.

“Ba za mu iya gina Nijeriya ko Afirka da muke zato ba tare da shigar da mata cikakken tsarin tattalin arzikinmu ba. Mata ba kawai masu shiga cikin tattalin arzikinmu ba ne; shugabanni ne, masu ƙirƙire-ƙirƙire, kuma ginshiƙin ci gaba mai ɗorewa,” inji mataimakin shugaban ƙasar.

A cewar ɓP Shettima, Project #SheIsIncluded an gina shi ne akan muhimman ginshiƙai huɗu na ilimi da ilimin kuɗi, kula da lafiyar mata, tsare-tsare masu ra’ayin jinsi, da faɗaɗa damar tattalin arziki ga mata.

Ya kuma bayyana cewa shirin zai kai ga dukkan ƙananan hukumomi 774 dake faɗin Nijeriya domin tabbatar da cewa babu macen da aka bari a baya.

“Alƙawarinmu na haɗa jinsi ba aikin kwaskwarima ba ne don sanya hankalin masu ci gaba; ginshiƙi ne na ci gaban ƙasa. Ba wai kawai muna tabbatar wa matan Nijeriya matsayinsu ba ne a tafiyarmu ta gamayya – muna samar musu da hanyoyin da za su jagoranci wannan muƙami,” inji Shettima.

Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa kwamitin shugaban ƙasa kan harkokin tattalin arziki da hada-hadar kuɗi tare da haɗin gwiwar ma’aikatar harkokin mata ne za su jagoranci shirin.

“Don gina tsarin tattalin arziki mai dunƙulewa inda duk ‘yan Nijeriya, ba tare da la’akari da jinsi ba, za su iya ba da gudummawa da kuma amfana, dole ne mu ruɓanya ƙoƙarinmu kuma mu daidaita da kyawawan ayyuka na duniya. Dole ne mu jajirce wajen cimma burinmu na ci gaba mai ɗorewa na 5— cimma daidaito tsakanin jinsi da kuma ƙarfafa dukkan mata,” inji shi.

Ya jaddada cewa taron na kwanaki biyu bai wuce taron tattaunawa ba domin hanya ce ta yin tunani sosai da kuma tsara dabarun gina ƙasa dunƙulalliya. Ya buƙaci masu ruwa da tsaki na gwamnati da masu zaman kansu da su yi amfani da damar wajen zayyana matakan da za a ɗauka don shiga cikin ajandar haɗa jinsi.

Shettima ya ƙara da cewa “Ina fatan shawarwarin da za su fito daga wannan taro, da sanin cewa za su tsara makomar haɗa jinsi a Nijeriya.”

A nata jawabin, shugabar alƙalan Nijeriya, Mai shari’a Kudirat Kekere- Ekun, ta ce taron wani muhimmin ci gaba ne a ƙoƙarin da ake yi na fayyace hanyoyin karya shingen ƙarfafawa mata da inganta hada-hadarsu.

Ta ce shigar da jinsi shi ne babban hanyar samar da ci gaba mai ɗorewa kuma jigon magance fatara da bunƙasar tattalin arziki, tana mai cewa kamata ya yi hakan ya zama ‘yancin kai na hada-hadar kuɗi, samar da arziki, da samar da jagoranci ga mata a ɓangarori daban-daban.

CJN ta ba da tabbacin cewa ɓangaren shari’a zai yi aiki tare da masu ruwa da tsaki don tabbatar da cewa an kare haƙƙoƙin mata na samun albarkatun tattalin arziki da mallakar dukiyoyi da dai sauransu ba tare da bin umarnin ɗaiɗaikun mutane ko tsofaffin al’adun gargajiya da ra’ayoyinsu ba.

A cikin wani saƙo da aka naɗa a wajen taron, mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar ɗinkin Duniya, Dakta Amina Mohammed, ta ce taron ya nuna wani muhimmin mataki na cigaban Nijeriya na haɗa jinsi, ƙarfafawa mata, da kuma ci gaba mai ɗorewa (SDGs).

Ta ce daidaito tsakanin jinsi da haɗa kai ba kawai burinsu ba ne, harsashi ne na samun ci gaba mai ɗorewa, zaman lafiya da ci gaba a faɗin duniya, ta kuma buƙaci kowa da kowa da ya saka hannun jari wajen ƙarfafa mata, inda ta yi nuni da cewa, idan aka ƙarfafa mata, al’umma za su ci gaba, tattalin arziki ya bunƙasa, al’ummomi kuma za su ci gaba.

Tun da farko, mataimakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa (Ofishin Mataimakin Shugaban ƙasa), Sanata Ibrahim Hassan Hadejia, ya ce goyon bayan da Shettima ke bayarwa da kuma ƙoƙarin ganin an samu ci gaba ya dace da duk wani abu da ya yi tun hawansa mulki, kuma shi ne jigon ajandar da za a bi wajen samar da ci gaba. Majalisar Tattalin Arziki ta ƙasa (NEC).

By ukarofi