Lokacin da za mu yaƙi maƙiya Kano ya zo – Gwamna Abba

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa, lokaci ya yi da za ta cigaba da yaƙi da masu hana jihar zama lafiya a duk inda suke, don ƙara dawo da matakin da jihar ta ke na cigaba.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da aikin titi mai tsawon kilomita tara a garin Zarewa da ke ƙaramar Hukumar Rogo.

Gwamnan Abba Kabir ya zare takobin da aka ba shi kyauta, domin nuni da ya shirya yaƙi tsaf, don yaƙar azzalumai maƙiya Jihar Kano da suka hana mutane zama lafiya.

Gwamna Yusuf ya kuma karɓi kyautar Alƙur’ani bugun hannu da kuma falleliyar takobi daga hannu Dr. Ishaƙ Falalu Zarewa a madadin al’ummar yankin bisa kammala aikin titin da ya ta shi daga Fulatan zuwa Zarewa da kuma wanda ya taso daga Danguzuri zuwa Zarewa.

Gwamna Yusuf ya ƙara da cewa, daga yau ya ɗaura ɗamara wajen yaƙi da cin hanci da rashawa, da zalunci da kuma cutar da al’ummar jihar Kano ta kowanne ɓangare.

Wannan dai shi ne karo na uku da gwamnan ya fito fili ya nuna shirinsa na yaƙar masu shirin tayar da fitina da rikici a jihar.

Wasu masu nazari na kallon kalaman nasa matsayin shaguɓe ga tsagin siyasar tsohon gwamnan jihar kuma shugaban babbar jam’iyyar adawa a jihar, wato APC, na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

By ukarofi