
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Alhamis ne lamarin ya auku da ɗaya daga cikin mambobin Majalisar Masarautar Zazzau mai suna Alhaji Rilwanu Yahaya Pate, wanda ya rasu a yayin da aka garzaya da shi asibitin Gambo Sawaba dake Zaria, Jihar Kaduna.
A wata sanarwa da majalisar ta fitar ta ofishin jami’in hulɗa da jama’arta, Abdullahi Aliyu Kwarbai, ta koka game da rashin Sarkin Yaƙin Zazzau, Alhaji Rilwanu Yahaya Pate.
Marigayin, wanda ya kuma taɓa riƙe muƙamin Mai kula da lamuran da suka shafi kiwon lafiya, ya rasu a yayin da ake tsaka da gudanar da wani taro a kusa da Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamali CFR.
An dai yi jana’izarsa ne a yammacin ranar a unguwar Rimin Dodo kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.
Mai Martaba Sarkin Zazzau a lokacin miƙa ta’aziyyar rasuwarsa marigayin, ya bayyana mutuwarsa a matsayin ƙaddara daga Allah da ka iya faruwa a lokacin da Ya so.
Ya kuma yi fatan samun haƙurin juriyar rashin ga iyalan marigayin da kuma cewa mutum ne jajirtacce kuma mai addini tare da yi masa addu’o’in fatan samun rahamar Allah SWT.
