
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnan Jihar Katsina, Umaru Dikko Raɗɗa ya buƙaci a rage adadin kwanakin dawowa gida ga mahajjata daga kwanaki 40 zuwa makonni uku ko huɗu.
Raɗɗa ya yi wannan kira ne a lokacin da Shugaban Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya kai masa ziyara a masaukin gwamnatin jihar dake Abuja.
Ya koka da yadda aka gudanar da harkokin aikin hajji a Katsina a shekarar da ta gabata ganin yadda aka fuskantaci ƙalubale da dama ciki har da rugujewar naira da ta haddasa tashin farashinsa.

A wata sanarwa da Sakataren yaɗa labaransa, Ibrahim Kaula Mohammed ya fitar, gwamnan ya ce lamarin hajji ya sanya maniyyata da dama cikin mawuyacin hali wanda har gwamnati ma sai da abin ya shafe ta, amma duk da haka sai da jiharsa ta tura mutane 2,700 zuwa hajji.
A yayin kalamansa game da kula da lafiyar maniyyata, Raɗɗa ya ce sun ɗauki matakan bada kariya a gare su, ya na mai kira ga NAHCON da ta riƙa ba su maganin cutar zazzaɓin cizon sauron kafin su bar Nijeriya.
Ya ƙara da cewa, Katsina ta bada tallafi ga mahajjatanta na shekarar 2024 – Naira miliyan 500 ga Hadya da kuma alawus na tafiya da adadinsa ya kai Dala 400 zuwa 500.
Gwamna Raɗɗa ya yi jinjina ga Gwamnatin Tarayya bisa sassauta farashin aikin hajji ta hanyar bada tallafi, ya na mai kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya cigaba da tallafa wa ɓangaren.
A ƙoƙarinsu na samar da rangwame ga mahajjata, Farfesa Abdullahi Saleh ya ce suna aiki tuƙuru da hukumomin Saudiyya inda ya ce a halin yanzu sun samu tallafin Naira biliyan 50 kuma suna fatan samun ƙari.
Ya ce kuɗin tafiya hajjin 2025 ya ragu daga N10m zuwa N8m inda kuma suna cigaba da tattaunawa don ganin an sake samun ƙarin ragin.
Farfesan ya kuma koka da wasu ƙalubale da NAHCON take fuskanta a inda ya bada misali da cajis da Bankin CBN ya cire na Naira biliyan 1.7 daga tallafin biliyan N90 da Gwamnatin Tarayya ta bayar a shekarar da ta gabata.
Kazalika, ya yi kira ga Gwamna Raɗɗa da ya taimaka wajen sanya ɗaukacin masu-ruwa-da-tsaki don samun sassauci game da harkoki da kuma farashin zuwa aikin hajji.
