
Daga BELLO A. BABAJI
Wani likitan zuciya ɗan kimanin shekaru 36 mai suna Ikenna Erinne ya kashe kansa biyo bayan wani hukuncin kotu a ƙarar da tsohuwar matarsa ta yi akan lamarin ɗaukar nauyin ɗa.
A ranar Lahadi, 26 ga watan Janairu ne al’amarin ya faru a Amruka.
Likitan, wanda asalin ɗan Jihar Anambara ne, sun rabu da matar tasa ne da jimawa, inda daga baya akan lamarin kula da ƴaƴa suka shiga rikicin da ya kai su zuwa kotu.
Ya yi rashin nasara ne a lokacin da kotun ta yanke masa hukuncin biyan Dala 15,000 a kowane wata don kula da ƴaƴansu.
Kamar yadda wani Clayton Udo, ɗan Nijeriya mazaunin Amurka ya wallafa a shafin X ya alaƙanta kisan kan da Erinne ya yi da matsalar kuɗi, ya na mai cewa ya kashe kuɗaɗe masu yawa wajen gudanar da shari’ar.
Haka kuma Erinne ya rasa lasisinsa na likitanci duk a yayin shari’ar, inda daga bisani ya harbe kansa.
