Ƙungiyar ma’aikatan lantarki za ta tsunduma yajin aiki a Kebbi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ƙungiyar ma’aikatan Wutar lantarki (NUEE), reshen jihar Kebbi ta koka da rashin kulawa da mambobinta yadda ya dace a bakin ayyukansu.

Haka kuma tsama da alaƙarta da hukumar gudanarwar lantarkin Kaduna, lamuran da suka haifar da ta yanke hukuncin shiga yajin aiki mara iyaka.

A wata sanarwa da Sakatarenta, Kwamared Salihu S. Shiru ya fitar a ranar 2 ga watan Fabrairu, ƙungiyar ta zayyano wasu ababe a matsayin dalilanta na tafiya yajin aikin.

Da farko ta ce akwai fansho na shekara biyar da ba a biya tsofaffin ma’aikata ba da kuma rashin biyan kuɗin ka’ida ga ma’aikatan da suka yi ritaya.

Haka kuma akwai rashin isasshen kayan aiki ga ma’aikata da kuma ƙin kara girma ga jami’an da suka cancanta.

Har’ilayau, Kwamared Shiru ya ce ba a aiwatar da biyan mafi ƙarancin albashi ba da aka amince da shi a shekarar 2024 da rashin biyan kuɗin ƙa’ida ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a bakin aiki da sauransu.

A saboda haka ne ƙungiyar ta yanke shawarar tafiya yajin aikin, wanda zai fara daga ranar 3 ga wata Fabrairu, 2025.

By Babaji