Matar Shugaba Tinubu ta ziyarci IBB da Abdulsalami a Minna

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Talata ne matar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Oluremi ta ziyarci tsofaffin shugabannin mulkin soja a Nijeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida da Janar Abdulsalami Abubakar a gidajensu dake Minna, Babban Birnin Jihar Neja.

Gwamnan jihar Umaru Mohammed Bago da matarsa Fatima Bago suka marabce ta a filin jiragen sama na Bola Ahmed Tinubu dake birnin da misalin ƙarfe 10:30 na safe.

Da fari dai Remi Tinubu ta je gidan IBB ne inda suka yi wata ganawar sirri ta tsawon mintina 35.

Matar Mataimakin Shugaban ƙasa, Hajia Nana Shettima ita ce wadda ta mara mata baya a yayin ziyarar.

Daga nan sai suka garzaya gidan Janar Abdulsalami, inda suka samu tarba ta karamci daga tsohon shugaban ƙasar. Ya nuna jin-daɗinsa ga ziyarar da suka kai masa.

Ziyarar ta tuna yadda Sanata Remi Tinubu ke ƙoƙarin ƙarfafa alaƙa da tsofaffin shugabannin Nijeriya da muhimmancin haɗin kan ƙasa da kuma girmama manyan ƙasa.

By Babaji