Daga AISHA ASAS
Gwamnatin Tarayya ta amince da kafa hukumar kula da basirar ƙirƙira da yawon buɗe-ido, wanda wani muhimmin shiri ne da aka tsara, domin haɓaka ƙarfin tattalin arzikin masana’antun ƙere-ƙere da yawon buɗe ido na Nijeriya ta hanyar haɗin gwiwa da hukumomi masu zaman kansu (PPP).
Ministar ƙirƙira, al’adu, yawon buɗe ido, da kuma tattalin arziki ta fuskar fasaha, Hannatu Musawa, ce ta bayyana hakan a ranar Litinin bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya, wanda shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a fadar shugaban ƙasa, Abuja.
Ta bayyana hakan a matsayin wani babban yunƙuri na sauya fasalin al’ummar ƙasar a ɓangaren ƙirƙira da fasara.
Musawa ta ce “Wannan shiri na da nufin ciyar da masana’antun ƙere-ƙere da yawon buɗe ido na Nijeriya zuwa wani sabon matsayi ta hanyar bunƙasa muhimman ababen more rayuwa da za su bunƙasa tattalin arziki na ciki da waje.”
A shekarar da ta gabata, a watan Oktoba na 2024, an dora wa Ma’aikatar fasaha, al’adu, yawon bude ido, da kuma bunƙasa tattalin arzikin ƙirƙira da fasaha, alhakin haɓaka fannin ƙirƙira tare da ba ta damar goyayya da takwarorinta na ƙasashen waje.
Musawa ta jaddada cewa, sabon kamfanin zai kasance a matsayin “abin hawa na musamman” da zai kai mu ga ganewa, cigaba, da kuma samar da kuɗaɗen shiga na musamman a ɓangarorin ƙirƙira da fasaha, da za su magance daɗaɗɗun matsalolin ɓangarorin.
“Sanannen abu ne yadda ƙirƙira da fasahar Nijeriya ke janyo hankalin ƙasashen duniya, kuma shugaban ƙasa na iya ƙoƙari wurin ba wa haɓaka ɓangaren ƙirƙira muhimmanci, wurin ganin duniya ba ta bar mu a baya ba a wannan ɓangare,” cewar Musawa.
Muhimman manufofin kamfanin samar da ababen more rayuwa na ƙere-ƙere da yawon buɗe ido sun haɗa da samar da dala biliyan 100 a ci gaban GDP da samar da ayyuka aƙalla miliyan biyu, musamman ga matasan Najeriya.
Abokan ci gaba da masu ruwa da tsaki daga ko’ina cikin duniya sun himmatu don tallafa wa sabbin abubuwan more rayuwa da hanyoyin samar da kuɗaɗen da ake buƙata don aikin.
Da take bayyana giɓin ababen more rayuwa da ke kawo tazgaro a ci gaban fannin, Musawa ta ba da misali da bukin “Detty December” da aka yi a Legas a watan Disamban da ya gabata, a matsayin misali na yadda Najeriya ke da ƙarfin ƙirkire-ƙirkire. “Ya kuke kallon irin cigaban da za a iya samu yayin da ire-iren waɗannan bukukuwa suka samu tallafin da suke buƙata,” inji ta.
An zayyana manya-manyan ayyuka da dama a ƙarƙashin shirin, waɗanda suka hada da: Samar da filin shaƙatawa na Abuja, faɗaɗa gandun dajin Yankari, gina birnin Abuja, wato ‘Abuja Creator City’ da gina sabbin sinima 5,000, da kafa cibiyar ƙirƙira ta Wole Soyinka ta Afrika, a Legas, cibiyar rarraba fasahar zamani ta ƙasa bakiɗaya.
Wani gagarumin aiki shi ne gina gidan tarihi na ƙasa a Abuja. Minista Musawa ta ce, “Babbar ƙasa kamar Nijeriya, wadda ta kasance uwa ga Afirka, amma a ce babu gidan tarihi a babban birninta ba, giɓin ne da muka ƙuduri aniyar cikewa.”
Shirin ya kuma haɗa da tsare-tsare na sanya Nollywood a matsayin wurin shirya finafinai a duniya da ƙirƙirar fagen waƙoƙi da zai yi goyayya da na ƙasashen da suka cigaba a fannin.
Musawa ta nuna kyakkyawan fata na nan gaba. “Wannan rana ce mai cike da alhairai ga harkokin yawon buɗe ido da masana’antu na ƙere-ƙere a Najeriya. Ta hanyar ɗinke gibin ɓangarorin ababen more rayuwa tare da samar da sabon tunani, za mu iya fahimtar darajar tattalin arzikin waɗannan sassa da kuma samar da fa’ida mai yawa ga al’ummar Najeriya.”
