Baɗala: Masarauta ta tuge sarautar Sojaboy bayan dakatarwar hukamar tace finafinai

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Masarautar Gidan Igwai ta Jihar Sakkwato, ta sanar da tuɗe mawaƙi Usman Umar, wanda aka fi sani da Sojaboy daga muƙamin da aka naɗa shi na Yariman Gidan Igwal.

Dalilin yanke wannan hukunci kuwa bai kaucewa irin wanda ya kai hukumar tace finafai dakatar da mawaƙin ba, wato yaɗa baɗala.

Idan mai karatu na bibiye da lamarin, a satin da ya gabata ne Humumar tace finafinal ƙarƙashin jagorancin Abba El-Mustapha ta dakatar da mawaƙi Sojaboy daga duk wasu harkoki da suka shafi Kannywood a Jihar Kano, sakamakon yaɗuwar wani faifan bidiyon waƙarsa da ya sanyawa suna ‘Bugun Zuciya’, inda yake rungumar wasu mata a ciki, wanda hakan ya saɓa wa addini da al’ada ta malam bahaushe.

Da irin wannan ne, masarautar ta ga munin abinda ya aikata har ta yi tir da shi, sannan ta aika masa da wasiƙar cire masa rawanin wadda ke ɗauke da sa hannun Alhaji Abubakar Marafa, a madadin Sarkin Adar Gidan Igwai.

“An umurce ni a madadin maigirma Marafan Gidan Igwai, domin in gabatar da wannan takarda ta dakatarwa da kuma tuɓewar ka daga sarautar Yariman Gidan Igwai, saboda yaɗa bidiyo mai cike da shagala, da rafkana, da baɗala, wadda ta saɓa wa addini da al’ada, da ɗabi’un unguwar Gidan Igwai, da al’ummar da ke cikin ta. Gundumar Gidan Igwal da ɗaukacin al’ummarta sun yi tir da Allah wadai da yaɗa wannan baɗala, akan haka suka barrantar da kansu daga wannan mummunar ɗabi’a da rashin dattako.

Muna addu’a da fatar za ka gyara, ka kuma saita dukkan lamurranka, a kan tarbiyya, da addini, da ɗabi’unmu na Musulunci. Wassalam,” inji saƙon takardar.

Daga ƙarshe takardar ta nuna an aika kofin takardar zuwa ga fadar Sarkin Musulmi, an kuma aika da wata a ofishin Hisba na reshen Jihar Sakkwato, da kuma ɗaya wadda aka aika wa ofishin Kwamishinan ‘Yansanda na jiha. An kuma kai wata a ofishin darakka na ‘yansanda masu farin kaya, wato DSS, da kuma wata a Hukumar Ciɓil Defence, sannan an kai wa Shugaban ƙaramar Hukumar Sokoto ta Arewa.

Yayin da yake mayar da martani, mawaƙi Sojaboy ya aika da saƙon amsa shi ma ta hahayar rubutacciyar wasiƙa, wadda ya rubuta da Ingilishi, kuma ya wallafa a shafinsa na Instagram. Wasiƙar wadda ke ɗauke da sunansa da kuma adireshinsa, mawaƙin ya amsa tuɓewar da aka yi masa daga sarautar Yariman Gidan Igwai, inda yake cewa, “Zuwa ga mai martaba Marafa, Sarkin Adar Gidan Igwai, Sokoto, Nijeriya. Wasiƙar amincewa tare da darajantawa. Tare da muntawa da aminci, na amince da hukuncin da sarki ya yanke. Na janye wa kaina matsayin Yarimar Gidan Igwai, na kuma karɓa da mutunci.

Ina miƙa godiyata ga mai martaba, da majalisar zartaswa kan damar da aka ba ni, ina fatan hikima nasara su jagorance goben wannan daular. Kuma a kodayaushe a shirye nake don ɗaukaka darajar masarautarmu mai girma. Tare da dukka girmamawa, Usman Sojaboy.Tsohon Yarimar Gidan Igwai, Shugaban kamfanin USB Entertaiment.”

Wannan dai bai kasance karo na farko da mawaƙin ya kawauce wa hanya ba, domin a baya ma wasu na yi masa kallon wanda ba Musulmi ba, ganin yadda yake kwaikwayon waɗanda suka barranta kansu da addinin islama, ta hanyar sanyo ababen da bahaushe ke kauce wa yin su a bainar jama’a, a ƙoƙarinsa na nuna shi ya waye.

By ukarofi