Daga IBRAHIM MIHAMMAD a Kano
Hajiya Amina Muhammad Babandede, yaya ga sabon Magajin Rafin Haɗeja da aka naɗa ta bayyana naɗin da aka yi wa ƙaninta Muhammad Babandede a matsayin Magajin Rafin Masarautar Hadeja da cewa abin farin ciki ne ga zuriyarsu bisa tabbatar musu da wannan sarauta da suka gada.
Ta bayyana haka ne da take zantawa da ‘yan jarida ta yi nuni da cewa tunda aka sanar musu an ba su wannan sarautar har an bayar da takarda suke ta ɗokin jiran ranar naɗin kullum tambaya suke yaushe ne? Ga shi Allah ya kawo lokacin ya nuna musu suna godiya ga Allah bisa wannan rana.
Hajiya Amina Muhammad Babandede ta ce su tsakaninsu da jama’a da yin hidima gare su abu ne da suka gada tun daga Madaki Ahmadu zuwa Madaki Sarkiki zuwa Muhammadu Babandede Sarkiki har zuwa kan shi da aka naɗa, kamar yanda mahaifinsu yake yana kwatanta hidima ga al’umma shima suna addu’ar Allah ya ƙara taimakonsu akan abinda ake a ƙara cigaba.
Ta ƙara da cewa babu abinda zasu cewa Sarkin Haɗeja domin abinda yayi musu na tabbatar da sarautar Magajin Rafi a gidansu, sai dai suyi masa addu’a tun daga kan mahaifinsa har zuwa kansa dama wata alaƙa ce ƙullalliya tsakanin mahaifinsu da mahaifinsa har kuma tazo da shi da babban wansu babban Kwanturolan na hukumar shige da fice mai ritaya Babandede saboda haka suna addu’a ga sarki kamar yadda suke yi wa iyayensu haka shi ma suke saka shi a ciki.
Hajiya Amina Muhammad Babandede ta jaddada cewa zuriyar gidan Muhammad Babandede gida ne na amsar baƙi suna da yawa kuma suna da mutane da suka zo daga sassa daban-daban da ƙauna ce tasa haka kuma suna fata yanda kowa ya zo lafiya Allah ya sa ya koma gidansa lafiya.
