Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da kwamiti da zai binciki ayyukan ƙungiyoyi masu zaman kansu

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

                                                                                                                                                                    

Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kwamitin musamman domin tantance ayyukan ƙungiyoyi masu zaman kansu (NGOs) da masu tallafi da ke aiki a jihar. Sakatare na gwamnatin jihar, Umar Faruk Ibrahim, ne ya jagoranci ƙaddamar da kwamitin, inda ya bayyana cewa matakin yana da nufin tabbatar da daidaito, tsaro, da dacewar ayyukan waɗannan ƙungiyoyi da manufofin ci gaban jihar.

A cewar SSG, kwamitin zai binciki dukkan kungiyoyi masu zaman kansu da ke aiki a Kano, tare da duba hanyoyin samun kuɗaɗen su, irin ayyukan da suke gudanarwa, da kuma yadda suke tafiyar da su. Haka nan, zai tsara hanyoyin da za su tabbatar da cewa ayyukan ƙungiyoyin sun yi daidai da dokokin jihar, tare da bayar da shawarwari kan yadda za a tsara dokoki don kare ƙungiyoyin a Kano.

Kwamitin yana da ikon dakatar da ayyukan kowace ƙungiya da aka samu tana aikata abubuwan da ba su dace ba ko kuma masu saɓawa da ɗabi’u da addinin mutanen jihar. Haka nan, zai iya shigar da ƙorafi ga hukumomin tsaro domin gudanar da bincike da kuma ɗaukar matakin doka kan ƙungiyoyin da aka samu da aikata ayyuka masu saɓa doka.

Shugaban kwamitin, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, wanda kuma shi ne kwamishinan yaɗa labarai da harkokin Clcikin gida na jihar, ya gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa amincewa da su. Ya tabbatar da cewa za su gudanar da aikinsu da gaskiya da adalci, tare da tabbatar da cewa duk wata ƙungiya da ke aiki a Kano tana tafiya daidai da ƙa’idojin jihar.

By ukarofi