Ni ke yi wa mijina komai duk da cewa ina aiki – Hannatu Muhammed

Spread the love

“Ba addinin da ya bai wa mata gata kamar Musulunci”

“Duk wadda za ta zuga ki ki yi wa mijinki rashin kunya ba mai son ki ba ce”

(Ci gaba daga makon jiya)

Daga UMAR GARBA a Katsina 

A satin da ya gabata, mun faro tattaunawa da jajirtacciyar ‘yar jarida, kuma shugabar ƙungiyar mata ‘yan jarida ta Jihar Katsina, wato NAWOJ. A tattaunawar mun taɓo ɓangarori da dama, wanda muka yada zango a tambayar da muka yi alƙawarin kawo maku amsarta kafin wasu su biyo baya. Har wa yau dai, wakilinmu a Katsina, Umar Garba ne ke jan ragamar tattaunawar. A sha karatu lafiya.

MANHAJA: Banda kasancewarki fitacciyar ‘yar jarida shin ko akwai wata sana’a da kike yi ta daban?

HANNATU: To gaskiya abinda ni ke yi shi ne aikin jarida sai kuma gwagwarmaya da ni ke yi, ni ‘yar gwagwarmaya ce ka gane, abubuwa da dama na faruwa da mata wanda mu da mu ka yi karatu dole ne mu taimake su don su fahimci me ye za su fuskanta a rayuwarsu, waɗannan abubuwan biyu su ne na sa a gaba sai dai ko nan gaba kasan idan kana aiki da gwamnati baza ka iya wani aiki ba amma ‘Actiɓism’ is allowed ( za ka iya yin gwagwarmaya).

Hajiya idan ba kya aikin komai wane abu ne kike yi don nishaɗantar da kanki?

Gaskiya abinda na fi yi idan bana aiki na kan kula da miji na saboda idan bana wajen aiki duk abinda ka sani nike yi wa mijina ni kan gaya wa mata wani lokaci idan sun kawo mana ƙorafi game da mazajensu, ina gaya masu cewa idan mijina nan hatta abinci nike girka ma shi kasan wasu sun kasa gane bambanci tsakanin ‘Actiɓism’ da kuma zama ‘responsible wife’ idan ke ‘yar gwagwarmaya ce ya kamata ki zama darasi ga waɗanda ke kusa da ke, amma wasu abinda suka ɗauka idan an ce ke ‘yar gwagwarmaya ce kin fi ƙarfin mijinki sai abinda kika ga dama za ki yi, ba haka ba ne idan ana maganar saka mata cikin gwamnati ko wajen bada muƙamai ba wai ana nufin kin fi ƙarfin mijinki ba, a’a ana nufin idan mu mata mun shiga don a dama da mu a aikin gwamnati za mu iya taimakon ‘yan uwanmu mata da ba su samu wannan damar ba wajen faɗin matsalolinmu har gwamnati ta ji kukanmu a biya mana waɗannan buƙatun na mu, ina yawan faɗa cewa duk duniya ba addinin da ya bai wa mata gata kamar addinin Musulunci, saboda idan wata ta kawo mani ƙorafinta idan na gane bata da gaskiya ni kan yi mata faɗa in ce ma ta bata kyauta ba kuma na kan ja hankalinsu akan kada su bari rayuwar wasu matan ta ruɗe su a shafukan sada zumunta irinsu Facebook, Instagram, TikTok da dai sauransu saboda haka idan na samu dama na kan faɗa wa mata cewa duk wata da zata zuga ki don ki yi wa mijinki rashin kunya gaskiya ba mai son ki ba ce.

Wacce shawara za ki bai wa matasa akan su tashi tsaye don su dogara da kansu?

Gaskiya akwai abubuwan da matasan yanzu ke yi da ke ci mani tuwo a ƙwarya, sai ka ga matashi ko matashiya ba su da aiki sai ɗora hotunan ‘yan siyasa a kafafen soshiyal midiya suna kambama su, abin takaici waɗannan ‘yan siyasar da matasan ke kambama wa sun gaza sama masu abin dogaro da kai, me ya sa baza ku yi amfani da kafafen sada zumunta wajen dogaro da kai ba?

Za ku iya yin tallace-tallace da sauran wasu abubuwan idan kana da followers (mabiya) da yawa akwai kafafe irinsu Facebook da za su riƙa biyanka kuɗi madadin ka yi haka ka zauna kana ɗaura hoton wani da ba kai yake tunani ba daga kanshi sai ‘ya ‘yanshi ya sani, amma kai baka tunanin yadda rayuwa ke tafiya karatu kaɗai bai isa ya ciyar da matashi ko matashiya gaba ba dole sai an haɗa da sana’a, kuma akwai sana’o’i da yawa da wayarka ma zaka iya yin aiki a biya ka.

Game da abinda ke faruwa da mata matasa sai dai a ce innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Za ka ga ɗiyar bahaushe Musulma tana abubuwan da ba su kamata ba ba ta tunanin goben ta duk abinda ka yi ‘posting’ yana nan a matsayin ‘record’ sai ranar da ka manta zaka gan shi ya sake dawowa daga baya kuma sai ka yi dana sanin ban yi ba, idan kin ga wata na yin shiririta a soshiyal midiya ba abin burgewa ba ne saboda ni kan ji ‘yan soshiyal midiyar na cewa ba sa iya auren waɗanda suke yin wannan abubuwan tare, saboda kowa na son mace kamila, mumina wadda idan ka aure ta kasan ba ka bar wa ‘ya ‘yanka wani tabo ba da za a ce ai da mamarsu ta yi abu kaza da kaza, saboda haka don Allah mu gyara. Amma za ka ga wasu tallar kayansu suke yi a waɗannan kafafe na soshiyal midiya ko awara kika riƙa yi kina ɗora wa ya fi maki yin raye-raye ko ɗora hotuna waɗanda ba su da wata rana da za su yi maki, saboda haka don Allah matasa mu yi amfani da soshiyal midiya ta hanyar da ta da ce.

Wane ƙalubale kike fuskanta wajen gudanar da ayyukanki?

E to ba za a rasa ƙalubale ba. ƙalubalen shi ne, wani lokaci ba ka da lokacin da za ka kula da iyalinka kamar yadda wasu suka sani aikinmu aiki ne mai wahala wanda ke buƙatar lokacinka ba hutu ba ‘weekend’ ko ‘public holiday’ sai an je aiki, shi ne babban ƙalubale. Sai kuma wani lokaci idan ba ka da lafiya sai a riƙa ganin ƙarya kike yi kawai kin kwanta gida ne ba kya son zuwa aiki wanda ba na tunanin za ka jawo wa kanka rashin lafiya saboda kana son ka zauna gida idan ba ka son zuwa aiki.

Ina kira ga shugabanninmu a wurin aiki su san cewar duk wata mace da suka gani a wurin aiki tana da rauni kuma akwai ɗawainiyar gida akanta abinda ake cewa, “What a man can do, woman can do better” ni dai ba na wannan layin gaskiya, amma zan iya yin abinda nasan zan iya yi.

Duk inda aka samu ƙalubale akan kuma samu nasarori. Waɗanne irin nasarori kika samu a rayuwa?

Alhamdulillah an samu nasarori, kuma duk nasarorin da na samu da farko ina gode wa mahaifina, saboda shi ne babban abokina duk duniyar nan, ina alfahari da duk abinda na zama, na zama saboda shi ne kasancewar ni ‘yar babanta ce, sai kuma mahaifiya ta da maigida na ina gode masu saboda da ban samu goyon baya daga mutanen nan uku ba, da ina iya ce maka nasarorin nan da ba su samu ba.

Maigida ina ƙara gode ma shi duba da yadda aikin nan ke ɗaukar lokacinmu da yawa, wani lokacin akan buƙaci ka tafi aiki wani wurin ba tare da an sanar da kai da wuri ba amma duk da haka ban fuskanci matsala daga wajen shi ba, shi ma ina gode ma shi kuma ina fata Allah ya saka ma shi da alkhairi ba don shi ba da ban zama abinda na zama ba a yau.

Hajiya mun gode ƙwarai da lokacinki da kika bai wa Blueprint Manhaja don yin hira da ke.

Ni ma na gode da kuka ga cewa na cancanta har ka ga za ka yi hira da ni. Ina maku fatan alkhairi.

By ukarofi