
Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon Kwamishinan Labarai na Tarayya kuma ɗaya daga cikin manyan ƙasa, Edwin Clerk ya rasu.
A wata takarda da iyalansa suka fitar, jagoran ƙungiyar mutanen yankin Neja-Delta ( PANDEF), ya rasu ne a daren ranar Litinin, 17 ga watan Fabrairu, 2025.
Marigayin ya rasu ne ya na da shekaru 97 a duniya.
Sanarwar ta kuma yi godiya ga al’umma bisa saƙon addu’o’i da suke aika masu.
Lamarin ya biyo bayan rasuwar Pa Ayo Adebanjo ne, wanda ya rasu ya na da shekaru 95, haka kuma shi ma ɗaya ne daga cikin manyan ƙasa daga yankin Kudu maso Yammacin Nijeriya.
