Majalisar Dokokin Jihar Edo ta amince da hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Majalisar Dokokin Jihar Edo ta yi kwaskwarima ga dokar hana garkuwa da ɗan-adam ta 2013, wadda ta bada damar tsare masu garkuwa da mutane na ɗaurin rai-da-rai.

Ƴan majalisar sun zartar da hakan ne a lokacin da suke nazarin ƙudirin dokar a ta 2025 inda suka amince da hukuncin kisa ga masu irin aikin.

Jagororin mafiya rinjaye da na marasa rinjaye sun amince wa kwamitin ƙudirin akan buƙatar sabon hukuncin.

Daga nan ne Kakakin Majalisar, Blessing Agbebaku ta umarci a kai wa gwamnan jihar kwafin takardun ƙudirin don tabbatarwa.

By Babaji