Akwai buƙatar koyi da shugabancin kasuwar Kantin Kwari – Auwalu Nice

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

An bayyana cewa akwai kyakkyawar buƙatar koyi da jagororin kasuwar Kantin Kwari tunda ga kan Manajan Darakta na kasuwar MD Sa’adu Dogon Nama da kuma shugaban ƙungiyar ‘yan kasuwar da ake kira Kantin Kwari Market Trader’s Association, Amb. ALGON Ishaƙ Alkasim Balarabe Tatari kan shirya gagarumin taro da nufin nemo hanyoyin sauƙaƙawa masu hayar gidaje da rumfuna a kasuwar ta hanyar ƙara wa waɗansu daga cikin masu sauƙaƙawa ‘yan kasuwar Kantin Kwari da kuma jawabai na wayar da kai kan muhimmanci yin hakan da ƙungiyar ta shirya ƙarƙashin shugabancin shugaban ƙungiya Alhaji Balarabe Tatari wanda aka gabatar a ranar Lahadi da ta gabata a ɗakin taron na Sani Abacha a Unguwar ƙofar Mata dake Kano.

Haka kuma Alhaji Auwalu Top Nice ya yaba wa MD Sa’adu Dogon Nama na cewa a matsayinsa na babban wakilin gwamna a kasuwar da ya jagoranci sauran shugabanni masu riƙe da muƙaman siyasa da na ƙungiya da ma dattawan kasuwar wajen ganin an samu ƙarin cigaba a wannan kasuwa ta Kwari mai albarka ta hanyar taimakawa ‘yan kasuwa da tallafi na bunƙasa kasuwancinsu da sauran shawarwari da za su taimakawa cigaban wannan kasuwa da kasuwancin Kano baki ɗaya bisa la’aƙari da yadda Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da mataimakin sa Kwaramade Aminu Abdulsalam da sauran jamian gwamnati Kano da al’ummar ta kauna yadda ta kamata.

Shi dai wannan taro ya samu halartar ɗimbin mahalarta da suka haɗa da ‘yan kasuwa Malamai da sauransu waɗanda suka gabatar da jawabi kaɗan daga cikinsu akwai Alhaji Auwalu Mai Tangaran wanda ya bayyana cewa wannan rana ran ace ta farin ciki kuma rana ce da suka ɗauki darasi da zasu cigaba da yin ƙoƙari abu yayi nasara wajen lalibo hanyar sauƙi ga ‘yan kasuwa Kantin Kwari Kano da Nijeriya baki ɗaya kamar yadda Alhaji Na Warure ya bayyana a wannan taro kaɗan daga cikin mahalarta taron akwai shugaban SIMDA Barista Junaidu da Sheikh Ibrahim Khalil wanda ya yi bayanin bayyana alheri a tsakanin al’umma na sa alheri ya yawaita a tsakanin al’umma da dai sauran ‘yan kasuwa, masana da malamai a wannan taro.

By ukarofi