Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Tun zuwan gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf aka dawo da karatu a Kwalejin Ilimi ta Gari da yanzu ta zama Yusuf Maitama Sule College of Education and Adɓance Studies dake ƙaramar Hukumar Ghari da gwamnatin baya ta Ganduje ta rufe da yanzu haka ana gudanar da muhimman ayyuka na gyaran makarantar gaba ɗaya domin kyautata yanayin koyo da koyarwa.
Shugaban Kwalejin Ass. Farfesa Abdullahi Asiru ya shaida wa ‘yan jarida hakan, inda ya ce suna yi wa Gwamnatin Abba godiya domin da farko ma shine ya sa hannu aka sauya sunan ƙaramar hukumar daga ƙunchi zuwa Ghari sannan ya sake buɗe makarantar da Kwankwaso ne ya ƙirƙirota ake karatun share fagen shiga jami’a da yin rimidiyal, amma gwamnati da ta gaje shi ta rufe.
Ya ce da Gwamna Abba ya zo ya ce ana so a samar da ƙwararrun malamai da za su koyar a makarantu aka sake buɗe makarantar da ɗaga likkafar ta da sauya mata suna ta zama na bada shaidar NCE da yin karatun sharar fagen shiga jami’a da na gyara jarabawa.
Ya ce bayan an buɗe makarantar an yi abubuwa na cigaba domin a da baya da aka gina ta ba katanga amma ana dawo da ita gwamna ya sa aka yi mata katanga aka zagaye ta aka yi mata babbar ƙofa ta shiga da fita da dakin masu gadi aka sa jami’an tsaro daban-daban da suke kula da tsaron makarantar aka kuma samar da malamai kwararru guda 91 da hukumar gudanarwa 10 yanzu suna da malamai da ma’aikata 101 da gwamnati ta sahale suke makarantar.
Farfsa Abdullahi Asiru ya ce yanzu haka ana ta gudanar da aiki a kwalejin ilimi na Yusuf Maitama Sule na Ghari babu dare ba rana kullum injiniyoyi da ma’aukata a can suka tare ana gyaran ajijuwa, rufi, kujeru, ofisoshi, ɗakunan kwanan ɗalibai da suka lalace lokacin da aka kulle makarantar a baya.
Ya ce akwai wuri na koyon sana’a da aka gina a baya na koyon ɗinki da yin sutura da Gwamnatin Kwankwaso ta gina a Ghari za su farfaɗo da ita domin koyawa yara sana’a domin su samu ilimi da kuma sana’a na dogaro da kai, kuma akwai rijiyoyin burtsatse huɗu na ruwan daɗi a makarantar da ake gyarawa yanzu haka hukumar samar da wuta a karkara ta Kano an basu umurni zasu sa baban tiransifoma sannan za a haɗa su da babbar layin samar da wuta ta ƙasa za a kuma sa fitilu masu aiki da hasken rana duk don inganta samar da wutar lantarki a kwalejin don kyautata tsaro.
Abdullahi Asiru ya ce a baya da aka rufe makarantar an bar ɗalibai yan wucin gadi da Makarantar CAS take kula dasu yan aji Biyu da yan aji Uku yanzu sun zo sun gaje su zasu kai guda 300 yanzu su kuma suna shirin ɗaukar sabbin ɗalibai sun buga fom guda 3,000 suna bada da su kyauta an zuwa daga ƙananan hukumomi 44 ana karɓa kyaut kowane ɗaya akan ₦5000 ya kama amma kyauta suke bayarwa don bada gudunmuwa ga manufar Gwamnati akan ilimi kuma suna sa ran zasu soma karatu da ɗalibai 1,000 domin akwai malamai da kayan aiki kuma zasu kiyaye tsari na addini da al’ada ɓangaren maza daban dana mata ba zasu yarda ayi zama na haɗaka ba sun kafa doka akai kowane aji ɓangaren maza daban dana mata don kiyaye mutunci da darajar da Allah ya yi wa ɗan adam.
Associate Farfesa Abdullahi Asiru ya ce yanzu haka kwalejin Ilimin ta Sule Maitama Yusuf ta Ghari nada tsangayoyi guda biyar da ɓangaren Ilimi,kimiyya,da koyon sana’oi da kuma “Art” sannan ƙarƙashin kowanne akwai sassa guda huɗu sannan wajen kwanan mata daban na maza daban da cikakken tsaro sun.kuma ware malamai mata huɗu da zasu kula da kare mutuncin ɗalibai mata, sannan a ɓangaren maza akwai malamai uku da aka sasu suna kula da maza sanan akwai masallaci da ɗakin cin abinci na ɗalibai da na kallo da wajen motsa jiki da wasanni har ma Kwamishinan matasa da wasanni Mustapha Rabiu Kwankwaso ya yi alƙawarin samar musu da kayayyakin wasanni na maza da mata.
