*Amurka ta jaddada taimaka wa Nijeirya a yaƙar Boko Haram
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Jakadan Amurka a Nijeriya, Mista Richard Mills, ya yi watsi da zargin da ake yi wa Hukumar Raya ƙasashe ta Amurka (USAID) tana tallafa wa ƙungiyar ta’addancin Boko Haram ko wasu ƙungiyoyin ta’addanci.
Mills wanda ya gana da mambobin aungiyar gwamnonin Nijeriya a Abuja ranar Laraba da daddare, ya ce babu wata shaida da ke tabbatar da zargin.
Ya bayyana cewa babu wata ƙasa da ta yi Allah wadai da ta’addancin Boko Haram fiye da Amurka, yana mai tabbatar da cewa idan aka samu wata shaida, gwamnatin Amurka za ta haɗa kai da gwamnatin Nijeriya domin gudanar da bincike.
“Babu wata shaida da ke tabbatar da zargin, kuma idan har muka samu shaidar cewa Boko Haram na yin amfani da kuɗaɗen shirinmu ta wata hanya da ba a sani ba, nan da nan za mu yi bincike tare da abokanmu na Nijeriya,” inji Mills.
“Muna ba da haɗkn kai wajen gudanar da bincike da gwamnatin Nijeriya. Ina mai tabbatar muku da cewa muna da tsare-tsare don tabbatar da cewa ba a karkatar da kuɗaɗen da hukumar ta USAID ko duk wani taimakon da Amurka ke bayarwa ba, ko daga USAID, ko ma’aikatar tsaro, ko ma’aikatar harkokin wajen Amurka, zuwa ga ƙungiyoyin ta’addanci irin na Boko Haram.
“Don haka, idan ana maganar Boko Haram, Amurka na goyon bayan Nkjeriya wajen son kawar da wannan bala’i da wannan ƙungiyar ke haifarwa.
“Bari na fayyace kowai — babu wata ƙawar Nijeriya da ya fi Amurka ƙarfi wajen yin Alla-wadai da ta’addancin Boko Haram da rashin mutunta rayuwar bil’adama kamar Amurka. Mun sanya 1ungiyar Boko Haram a matsayin ƙungiyar ta’addanci ta ƙasashen waje tun shekarar 2013, tare da hana ƙungiyar miƙa kadarori ga Amurka tare da ba mu damar kamawa tare da kama mambobinta.”
A ranar 13 ga watan Fabrairu, ɗan majalisar dokokin Amurka, Scott Perry, ya zargi hukumar ta USAID da tallafa wa ƙungiyoyin ta’addanci ciki har da Boko Haram.
A wani ci gaban kuma, Amurka ta yi Allah-wadai da ayyukan ƙungiyar ta’addanci ta Boko Haram, inda ta ce za ta ci gaba da haɗa kai da Nijeriya da yankin ta duk hanyar da ta dace wajen tsaron lafiyar al’ummarta.
wata sanarwa da ofishin jakadancin Amurka ya wallafa a shafinsa na Tiwita, Amurkar ta yi Alla-wadai da ayyukan ƙungiyar Boko Haram da sauran ƙungiyoyin ta’adda a Nijeriya da sauran ƙasashen Afirka.
Sanarwar da ƙara da cewa, “a 2013 ne dai Amurka ta ayyana ƙungiyar Boko Haram a matsayin ƙungiyar ’yan ta’adda, inda ta rufe duk waɗansu kadarorin da ƙoƙorinta na neman gidauniya da kuma gurfanar da mambobinta tare da hana su tafiye-tafiye zuwa Amurka.”
Ofishin Amurkar ya kuma ce ƙasar Amurka na ci gaba da aiki tare da Nijeriya da sauran ƙasashen Afirka wajen yaƙar ayyukan ta’addanci.
A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne dai wani ɗan majalisar dokokin Amurka, Scott Perry, ya bayyana cewa hukumar raya ƙasashe ta Amurka, USAID ce ke samar wa ƙungiyoyin ta’adda da suka haɗa da Boko Haram kuɗaɗe.
Perry wanda ya yi batun lokacin wani sauraron rahoton kwamitin majalisar a kan yadda hukumomin gwamnatin Amurka ke aiwatar da ayyuka da sarrafa kuɗaɗe tun bayan da shugaba Donald Trump ya ce bai ga amfanin hukumar ba.
Wannan ne ya sa wasu daga cikin ’yan majalisar dokokin Nijeriya ɗaukar matakin gabatar da ƙudiri a gaban majalisar dokokin ƙasar.
