
Daga BELLO A. BABAJI
Jaridar ‘New Telegraph Nigeria’ ta karrama Gwamna Abba Kabir Yusuf Jihar Kano, a matsayin gwamnan da ya fi kowane gwamna a Nijeriya ƙoƙari a ɓangaren bunƙasa harkar ilimi a jiharsa.
Kakakinsa, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya bayyana hakan a wani saƙo da ya aika wa manema labarai, inda ya ce mawallafin jaridar kuma tsohon gwamnan Jihar Abia, Sanata Orji Uzor Kalu tare da tsohon gwamnan Jihar Edo, Adams Oshiomhole ne suka gabatar masa da kyautar karramawar.
Ya kuma ce, wasu daga cikin manyan ƙasa da suka halarci taron miƙa kyautar akwai Shugaban Kamfanin Man fetur na Ƙasa, NNPCL, Mele Kyari da sauransu.
Hakan ya nuna yadda Gwamna Abba na jam’iyyar NNPP ke aiki tuƙuru wajen ganin gwamnatinsa ta inganta harkar ilimi a Kano.
Mai taimaka masa na musamman akan harkokin jihar, Usman Bala shi ne wanda ya wakilce shi a wajen karramawar.
