
Daga BELLO A. BABAJI
A ƙasa da kwana ɗaya kwafin litafin rayuwar tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) mai suna ‘A Journey in Service’, ya karaɗe kafafen sada zumunta.
A kafar X, wanda da aka sani da Twitter, an yi ta yaɗa adireshinsa wanda ya sanya masu manhajar ke rububin ɗauka ta kafar a madadin sayen kwafin bugun littafin a kasuwa.
Haka ma a kafar Wattsapp an yi ta yaɗa shi a guruf-guruf a tsakanin mambobi ta salon adireshi da tsarin PDF.
Lamarin da ya sanya ƴan kasuwar wallafawa da sayar da litattafai kokawa ganin yadda mutane da yawa suka mallaki littafin ta kafafen sadarwa.
A ranar Alhamis ne ya ƙaddamar da littafin a Abuja, inda wasu daga cikin tsofaffin shugabannin Nijeriya da wasu manyan ƙasa suka halarta.
Shugaba Bola Tinubu ya halarci taron a matsayin babban baƙo na musamman, sai tsohon shugaban ƙasar Ghana Nana Akuffo-Addo, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo da dai sauransu.
Zuwa lokacin kammala rahoton, IBB bai ce komai ba game da batun.
