NAFDAC ta ƙaddamar da shirin “Catch Them Young” a makarantun Gombe

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) ta ƙaddamar da ƙungiyar tsaron masu amfani da kayayyaki (Consumer Safety Club) a makarantar sakandare ta ‘yan Mata, Kaltungo, domin yaƙi da matsalar shaye-shaye da wayar da kan ɗalibai kan magunguna na bogi da kayan abinci marasa inganci.

Wannan shiri mai taken “Catch Them Young” yana nufin wayar da kan matasa kan illolin amfani da miyagun ƙwayoyi, magunguna na jabu, da kayan abinci marasa lafiya, tare da koya musu mahimmancin rayuwa cikin lafiya da tsaro.

Jihar Gombe ce aka zaɓa a matsayin wakiliyar shiyyar Arewa maso Gabas don gudanar da shirin, wanda zai shafi makarantun sakandare guda shida a jihar.

Da take gabatar da jawabi a wajen ƙaddamarwar, Ko’odinetan NAFDAC na Jihar Gombe, James Agada, wanda ya wakilci babbar daraktar NAFDAC, ta ƙasa Farfesa Mojisola Adeyeye, ta yi kira ga ɗalibai su guji tasirin abokan banza da kuma shaye-shaye.

“A guji tasirin abokan banza. Kada ku bari halayen shaye-shaye su kama ku. Shaye-shaye suna lalata rayuwar mutane, suna jawo ƙwayoyi, rashin lafiya, da manyan laifuka kamar fyade da kisan kai,” inji Agada.

Ya kuma yi kira ga malamai su zama jagorori na gari ga ɗalibai, tare da bayar da goyon baya a lokacin da suka lura da halayen da ba su dace ba.

“Malamai suna da rawar gani wajen gano ɗabi’un da za su iya jefa ɗalibai cikin matsala. Idan ɗalibai ba za su iya magana da iyayensu ba, kamata ya yi su sami damar tattaunawa da malamansu don samun jagoranci,” inji shi.

Mataimakin darakta na NAFDAC, Musa Haruna, ya gabatar da takarda mai taken “Muhimmancin Ƙungiyar Tsaron Masu Amfani da Kayayyaki (NCSC)”, inda ya yi bayani kan nasarorin da hukumar ta samu wajen rage yawaitar kayayyaki marasa inganci tun daga kafuwar ƙungiyar a shekarar 2012.

Ya bayyana cewa wannan shiri ya taimaka wajen wayar da kan ɗalibai game da muhimmancin kiyaye lafiyarsu da kuma bayar da gudummawa wajen kawar da kayayyakin da ba su da inganci a cikin al’umma.

Shugabar Makarantar Sakandaren ta ‘yan mata na, Kaltungo, Hajiya Fati Ishiaku Awak, ta yaba wa NAFDAC kan wannan gagarumin shiri, tana mai alƙawarin tabbatar da ɗorewarsa a makarantar.

“Wannan shiri ya zo a lokacin da ya dace, kuma yana matuƙar muhimmanci. Za mu ci gaba da wayar da kan ɗalibai kan wannan batu, kuma za mu ɗauki matakan da suka dace don tabbatar da an cimma burin shirin,” inji ta.

Wannan shiri na NAFDAC ya kasance wani muhimmin ɓangare na yaƙin da ake yi da matsalar shaye-shaye a tsakanin matasan Najeriya, tare da nufin tabbatar da lafiyar jama’a da tsaron rayuwa.

By ukarofi