Majalisar Wakilai ta ƙi amincewa da buƙatar kafa sababbin jihohi 31

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Kwamitin Majalisar Wakilai kan Gyare-gyaren Dokoki ya ƙi amincewa da duka buƙatun da ke neman a kafa wasu sabbin jihohi a Nijeriya da aka gabatar wa Majalisar.

A ranar 6 ga watan Fabrairu, 2025 ne aka gabatar mata da buƙatun.

Daga cikin jihohin da ake neman a samar akwai Ibadan, Ijebu, Savannah da Etiti da sauransu.

A lokacin da ya ke magana a Uyo, Jihar Akwa-Ibom, Shugaban kwamitin kuma Mataimakin Kakakin Majalisar, Benjamin Kalu ya ce duk da cewa buƙatun sun dace da manufofin shiyyoyin Nijeriya, babu ɗaya da ya cike sharuɗɗan da ake buƙata na kafa jiha, kamar yadda sakin layi na 8 na kundin 1999 na Dokokin ƙasa ya bayyana.

Ya ce, kwamitin zai ƙara wa’adin amsar buƙatun la’akari da yadda tattaunawar batun ta kasance a ƙoƙarinsu na cimma matsaya.

Ya kuma ce, a halin yanzu kwamitin na ƙoƙarin yin gyara ga dokoki guda 151 a ƙarƙashin ƙudirorin gyaran doka.

Daga cikin su akwai batun tsarin tarayya, ƴancin cin gashin kai, kasafin kuɗi, gyaran zaɓe, tsaro, ƴancin ɗan-adam da sauran su.

Ya tabbatar da cewa, za su yi gyare-gyaren ne la’akari da maslahar ƙasa da ta al’umma don cimma nasara.

By Babaji