Burinmu mu haɗa ‘yan Tiktok na Arewa da ƙungiyoyi da hukumomi don a tallafa musu – Sharfudden Bature

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Sabuwar ƙungiyar wayar da kai da cigaban al’umma ta kafafen sada zumunta na Tiktok, wato Social Media Awareness and Promotion Deployment Association SMAPDA ta gudanar da taron wayar da kai ga membobinta na jihahi 19 da ke Arewacin Nijeriya.

Babbar manufar taron dai shi ne ilmantar da matasan arewa masu ta’amulli da kafar sadarwa ta Tiktok.

Taron wanda shi ne irinsa na farko a arewaci an gudanar da shi a ranakun Juma’a da Asabar a hotel din Bristol Hotel da ke, Kano.

Sharfudden Bature wanda shi ne sakataren ƙungiyar ya bayyana cewa, Allah ya yi wa Arewa baiwa kala-kala wanda suke amfani da Tiktok wajen nuna baiwar su, amma ana yin abin ne a banzace ba shi da kima.

“Matasan nan ba sa amfana da kafar yadda ya kamata, a wasu lokutan ana ɓata al’adun da addini saboda haka ya sa muka ƙirƙiri wannan ƙungiyar ta ƴan Tiktok, mu haɗa kanmu wuri ɗaya, kuma za mu sanar da su su waye su, sannan mu haɗa su da ƙungiyoyi da hukumomi da za su taimake su, kuma su ma yaran su taimaki kansu.

Idan har yaran nan suka sami ilimi za’a iya amfani da su wajen wayar da kai, wajen kasuwanci, bunƙasa al’ada da addini.

Muna son ƙungiyar ta zama wata babbar rumfar tura saƙonni na mutunci da kirki”. inji Bature

Ɗaya daga cikin membobin wannan ƙungiya kwamarad Sai’du Zahra’u Mustapha da take amfani da take amfani da Misis Zahra. Wacce mai bada dariya ce ta kafar Tiktok ta ce zuwanta taro ta ƙaru matuka, domin ta haɗu da mutane da dama waɗanda a da ba su santa ba, ita ma ba ta sansu ba, amma yanzu an ga juna.

Ta ƙara da cewa ” za mu baiwa shugabanninmu haɗin kai domin dama in dai ka ga ana abu kara zuɓe to rashin haɗin kai ne, in dai an samu haɗin kai to komai ma za a same shi” inji mis Zahra.

Bincike ya nuna cewa ƴan Nijeriya sun fi amfani da kafar sadarwa ta Tiktok a kan kafafen sada zumunta inda aka ƙiyasta cewa, matasa Miliyan 23 ne suke amfani shi.

Yayin da mutane Miliyan 15 suke amfani da Tiktok a jahohi 19 na Arewacin Nijeriya.

By ukarofi