
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Juma’a ne Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna (NAFDAC), ta gano wasu shagunan sayar da kayayyakin gine-gine ɗauke da wasu magungunan bogi a wata kasuwar magunguna a Birnin Onitsha dake Jihar Anambara.
NAFDAC ta fara gudanar da atisayen ne a ranar 10 ga watan Fabrairu, 2025 a ƙoƙarinta na tsaftace Nijeriya daga amfani da magungunan da wa’adinsu ya ƙare.
Lamarin da ya sanya ta yi nasarar tara tireloli 10 ɗauke da gurɓatattun magunguna da ake ƙoƙarin yaɗa su acikin al’umma.
Wakilin Blueprint ya ruwaito cewa, jami’an NAFDAC sun yi nasarar ƙwato gurɓatattun magunguna da na bogi waɗanda adadinsu ya kai cikin tirela biyu a yayin atisayen da suka gudanar a kasuwar.

Darakta-Janar ta hukumar, Farfesa Moji Adeyeye, wadda Daraktan Shiyyar Kudu maso gabas, Dakta Martins Iluyomade ya wakilce ta, ta ce ta yi mamakin ganin yadda wasu mutane ke amfani da shagunan kayan gini a matsayin wajen ɓoye magungunan bogi.
Ta ce, mafi yawancin ƴan kasuwar da aka kama sun yi ta musanta batun da cewa ba su san takwarorinsu suna gudanar da harƙallar gurɓatattun magungunan ba.
Ta ƙara da cewa, za su cigaba da gudanar da atisayen don tabbatar da tsare al’umma daga amfani da ire-iren magungunan da wasu lalatattun mutanen ke yaɗawa acikin ƴan Nijeriya.
