Duk da kashedin Ministan Shari’a da ‘yan sanda, zaɓen ƙananan hukumomi ya gudana a Osun

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

An gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a Jihar Osun kamar yadda aka tsara, duk da kiran da ministan shari’a na tarayya da rundunar ‘yan sanda suka yi na dakatar da shi. Gwamna Ademola Adeleke ya kaɗa ƙuri’arsa a ƙaramar hukumar Ede North, inda ya yaba da zaman lafiyar da aka gudanar da zaɓen, yana mai kira ga jama’a su fito su kaɗa ƙuri’a cikin lumana.

Babban Lauyan Tarayya, Lateef Fagbemi, ya buƙaci dakatar da zaɓen bisa hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ya ce ya mayar da shugabannin ƙananan hukumomin jam’iyyar APC da aka tsige a baya. Haka zalika, rundunar ‘yan sanda ta ce tana da rahotannin sirri da ke nuna yiwuwar tashin hankali da barazana ga tsaro idan aka ci gaba da zaɓen.

Duk da haka, gwamnatin Osun ta dage cewa dole ne a gudanar da zaɓen domin bin umarnin kotu. Kwamishinan watsa labarai na jihar, Kolapo Alimi, ya ce gwamnati ba za ta saɓa wa doka ba, yana mai sukar matakin ‘yan sanda da ya ce yana da nasaba da siyasa.

A halin da ake ciki, babbar jam’iyyar adawa ta APC ta janye daga shiga zaɓen. A yayin da wakilinmu ya zagaya babban birnin jihar, Osogbo, ya lura da cewa gari ya kasance cikin kwanciyar hankali, kasuwanci ya tsaya cak, sai dai an ga ‘yan sanda a tituna don tabbatar da tsaro.

By ukarofi