Kotu ta bada belin Farfesa Usman Yusuf

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wata Babbar Kotun Taraya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon Babban Sakataren Hukumar Inshorar Lafiya ta Nijeriya (NHIA), Farfesa Usman Yusuf, wanda ya ke fuskantar tuhume-tuhumen aikata almundahana.

A jiya Alhamis Mai Shari’a Chinyere Nwecheonwu ta bayar da umarnin sakin Farfesa Yusuf daga gidan kurkukun Kuje bayan cika ƙa’idojin belin.

Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati ce ta gurfanar da Farfesa Yusuf a bisa wasu tuhume-tuhume guda biyar masu nasaba da zargin almabazzaranci da bai wa kansa damar da bata dace ba a matsayinsa na shugaban NHIS a 2016 ta hanyar amincewa da sayen motoci akan Naira miliyan 49, 197, 750 saɓanin Naira miliyan 30, 000, 000 da aka kasafta kashewa.

EFCC ta kuma yi zargin cewar Farfesa Yusuf ya samu wata dama ta kashin kai a wani kamfani mai suna “Lubekh Nigeria Limited” ta hannun wani ɗan ɗan uwansa, Khalifa Hassan Yusuf, inda ya ba shi kwangilar yaɗa labarai da hulɗa da jama’a ta Naira miliyan 17.5.

Wanda ake tuhumar ya ƙi amsa laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa.

By ukarofi