Kotu ta wanke Naira Marley, Sam Larry, Primeboy daga zargin kisan Mohbad

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Wata Kotun Majistare da ke zamanta a unguwar Sabo da ke Yaba a Jihar Legas, ta wanke fitaccen mawaƙi Azeez Fashola, wanda aka fi sani da Naira Marley, da wasu mutane uku daga hannu a rikicin mutuwar ɗan uwan sana’arsu, Aloba Oladimeji lleri-Oluwa, wanda aka fi sani da Mohbad.

Alkalin kotun Ejiro Kubenje, wanda ya jagoranci shari’ar a ranar Talata, ya aiwatar da shawarwarin lauyoyi daga hukumar kula da kararrakin jama’a (DPP) da ke Legas, inda ta bayyana cewa Naira Marley ba ya da wata tambaya da zai amsa dangane da rasuwar Mohbad.

Baya ga Naira Marley, kotun ta ce ta saki wani mai shiryawa waka, Samson Balogun, wanda aka fi sani da Sam Larry; Owodunni Ibrahim, wanda kuma ake kira Primeboy; da kuma tsohon manajan Mohbad, Opere Babatunde.

By ukarofi