Jami’ar Tarayya ta FUTD da Team Nig sun wayar da kan ma’aikata da ɗalibai dabarun sufuri a Katsina

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau 

Jami’ar Sufuri ta Tarayya, dake Daura (FUTD) tare da haɗin gwiwa da Kamfanin Technic, Engineering, Architecture and Marketing (TEAM), Nig. Ltd. sun gudanar da taron ƙarawa juna sani na kwanaki biyu ga ma’aikata, ɗalibai da sauran jama’a kan bunƙasa dabarun sufuri a zamanance.

A cewar jami’in yaɗa labarai na Jami’ar Umar Usman a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Gusau ranar Laraba ya bayyana cewa taken taron shi ne “tsare-tsare, ci gaba da sarrafa ababen more rayuwa na sufuri a Nijeriya”.

Shugaban Jami’ar, Hon. Farfesa Umar Adam Katsayal a nashi jawabin, ya yabawa kamfanin gine-gine na ƙasar Sin (CCECC) ta hanyar samar da gine-gine a jami’ar.

Ya kuma buƙaci sauran kamfanoni da ke aiki a Nijeriya da su yi koyi da CCECC da TEAM wajen tabbatar da bunkasa Corporate Social Responsibility (CSR).

Da yake magana game da TEAM a matsayin kamfani da ke aiki a Nijeriya, shugaban Jami’ar ya bayyana cewar, kamfanin ya bayyana cewa kamfanin yana da ƙarfin ma’aikata kusan 400 kuma ya samu ci gaba cikin sauri tun shekaru tamanin.

Shugaban tawagar TEAM Nig. Ltd., Engr. Precious Ebare, wacce ita ce Manajan aikin da ke kula da hanyar jirgin kasa daga Kano zuwa Kaduna, ta bayyana cewa TEAM “kamfani ne mai ba da shawara kan injiniyanci na TEAM Group”.

“TEAM tana ba da shawara ce ta shahara a duniya wacce ta kware a fannin injiniya, tsara birane da gine-gine, tare da manyan ofisoshi a nahiyoyi uku.”

A cewarta, ci gaban ƙungiyar ya fara ne a shekarar 1975 tare da kafa T.E.A.M., sannan a shekarar 1977 TEAM Engineering, kamfanin da aka ba wa amana ta musamman wajen aiwatar da zane-zane a ɓangarori daban-daban na injiniya, gine-gine da tsara birane.

Malam Talha Ali, Injiniyan Lantarki a cikin jawabin sa ya bayyana mahimmancin ababen more rayuwa na sufuri, inda ya bayyana cewa yana tallafawa ci gaban tattalin arziki, haɗin kai, da walwala.

A cewarsa, tasirin tattalin arziki na ababen more rayuwa na sufuri sun hada da saukaka kasuwanci da bunƙasuwar kasuwanci da inganta cuɗanya tsakanin birane da ƙasashe.

Da yake gabatar da jawabi, Izomoh Akposiri, Injiniya Material ya yi magana kan layukan dogo a Nijeriya inda ta yi magana kan ƙididdiga kan ababen more rayuwa na sufuri a duniya musamman Nijeriya.

A yayin da yake magana kan tarihi da cigaban hanyoyin jiragen kasa na Nijeriya, Akposiri ya ce an gina layin dogo na Nijeriya tsakanin shekarar 1898 zuwa 1964, wanda ya kai kilomita 3,505 na layin dogo na Narrow-Gauge.

Ya kuma bayyana cewar an gano nau’o’in ma’auni daban-daban a duniya da suka hada da Broad-Gauge, Standard Gauge, Meter Gauge da Narrow Gauge.

Haka nan, Arc. Mubarak Mustapha da Mista Olusegun Adebisi sun bayani ne a kan zane-zanen gine-gine na tashoshin jiragen kasa da kuma rawar da kamfanonin injiniya ke takawa a masana’antar gine-gine.

Engr. Precious Ebare da Izomoh Akposiri sun kara yin tsokaci kan tsare-tsare da bunkasar hanyar jirgin kasa, inda suka bayyana mahimmancin nazarin yiwuwar yin aiki da nazarin tasirin muhalli da zamantakewa.

Jaridar Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa an kara sanar da daliban FUTD cewa, kasancewar su daliban jami’ar sufuri ta farko a Nijeriya da Afirka, suna da wata dama a gaban su a Nijeriya musamman ma idan za su iya nuna kimar su wajen fasahar sufuri.

An yi kira ga daliban da su mike tsaye don neman ilimi ba wai su dogara kacokan kan laccocin ajujuwa ba sai dai su kasance masu taka rawa a harkokin sufuri.

Da yake gabatar da jawabin godiya, Daraktan Tsare-tsare na Ilimi, Farfesa Ahmad Abubakar ya yabawa Hukumar Gudanarwar Jami’ar, musamman Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Umar Adam Katsayal, bisa yadda yake tallafa wa horar da ma’aikata da tsare-tsare na ci gaba ilimi.

Daga ƙarshe ya buƙaci ƙungiyar ta TEAM Nig. iyakance don kiyaye dangantakar da Jami’ar, tare da tabbatar da cewa Jami’ar za ta yi hakan.

By ukarofi