Natasha ta nemi a tafka mahawarar binciken ta a bainar jama’a

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Sanatar da ke wakiltar Jihar Kogi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Natasha Akpoti-Uduaghan ta haƙiƙance akan sai dai a gudanar da binciken ta ta hanyar haska wa al’umma kai-tsaye.

Ta ce, ƴan Nijeriya suna da ƴancin su shaida al’amarin.

A wani saƙo da aka wallafa a ranar Alhamis ta soshiyal mediya, Natasha ta ce da farko an hana ta magana a fili game da batun da wasu batutuwan majalisar, amma yanzu ta zaɓi ta bayyana wa al’umma.

Ta yi kira ga ƴan Nijeriya da su bibiyi al’amarin don tabbatar da an yi adalci.

Ta kuma wallafa ƙarar da Ƙungiyar Matasan Arewa ta NOYAD ta shigar akan ta, wanda ke neman a yi bincike akan ta da hukunta ta akan hannu a rashawa.

Saidai duk da haka, Akpoti-Uduaghan ta nemi a gayyace ta a wani gidan talabijin na ƙasa don a tattaunawa da ita akan lamarin.

By Babaji