
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Filato ta ce ta ɗauki matakin dakatar da haƙar ma’adanai ne don tsare rayuka da dukiyoyin ƴan jihar.
Kwamishinan Kula da Muhalli da Sauyin Yanayi da Ci-gaban Albarkatun ƙasa, Peter Gwom ya bayyana hakan a taron manema labarai a Jos, ranar Alhamis.
A ranar 21 ga watan Fabrairu ne Gwamna Caleb Mutfwang na jihar ya umarci a dakatar da ayyukan haƙar ma’adanai a jihar bisa dalilan tsaro.
Ya kuma kafa kwamiti ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Shari’a, Philemon Dafi don tabbatar da an kiyaye umarnin nasa.
Mista Gwom, wanda ya yi magana a madadin kwamitin, ya bayyana cewa, akwai barazanar tsaro game da ayyukan haƙar waɗanda ke sanya yankunan da ake yin su cikin haɗari.
Ya ce, Filato ita jihar da ke kan gaba wajen ayyukan haƙar ma’adanai a Nijeriya tun daga shekarar 1902.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su daina siyasantar da al’amarin ganin yadda matakin ya zama abinda zai amfani ƴan jihar baki ɗaya.
Haka kuma buƙaci al’umma da su kiyaye umarnin, wanda hakan zai taimaka wajen daƙile ayyukan ta’addanci a jihar da kuma janyo ra’ayoyin masu zuba jari kan sahihancin ayyukan gwamnatin jihar.
