
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu a kasafin kuɗi na shekarar 2025, wanda adadinsa kai Naira tiriliyan 54.99.
Tinubu ya yi hakan ne a idon jagororin majalisun dokoki da wasu manyan jami’an gwamnati a ofishinsa dake Fadar Shugaban ƙasa a Abuja.
A ranar 14 ga watan Fabrairu ne ƙudirin kasafin ya tsallake karatun tantancewa daga majalisun Dattawa da wakilai bayan Shugaba Tinubu ya nemi a yi ƙari kan tiriliyan N49.7 da ya gabatar a karon farko.
Majalisa ta amince ne da kasafin, wanda ya haura tiriliyan 54.2 da Shugaban ƙasar ya buƙaci ta amince da shi a lokacin da ya nemi ƙarin.
Ƙarin ya biyo bayan hoɓɓasa ne da Hukumomin tattara kuɗaɗen haraji (FIRS) da Kwastom suka yi na samun ƙarin kuɗaɗen.
Kasafin zai warware matsalolin ɓangarorin da suka shafi tsaro, ababen more rayuwa, ilimi da lafiya, wanda za a ware Dala miliyan 200 don maye giɓin da aka samu a kwanan nan kan rasa tallafin kiwon lafiya na Amurka.
Bugu da ƙari, Gwamantin Tarayya za ta yi ƙoƙarin samar da rangwame ga kuɗin Dala, wanda ya kai N1,500 da manufar rage hauhawarsa daga kaso 34.8 zuwa kaso 15 a cikin shekarar.
Kasafin 2025 ya nuna cewa an samu ƙari akan tiriliyan N27.5 na 2024 da kaso 99.96.
