Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Darakta Janar na Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta ƙasa (NOA), Mallam Lanre Issa-Onilu, a ranar Juma’a, ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su yi hattara da illolin zazzaɓin Lassa.
Mallam Issa-Onilu ya bayyana haka ne a wani taro na birnin tarayya domin fara gangamin wayar da kan jama’a domin daƙile yawaitar cututtuka masu saurin yaɗuwa da ke addabar wasu jihohin ƙasar nan.
Daraktan NOA na ƙasa ya, wanda ya samu wakilcin Shugaban Kula da Lafiya da Zamantakewa, Dokta Olufemi Ayoola, ya sanar da cewa, har yanzu muna lokacin zafi, lokacin da ake fama da cutar zazzaɓin Lassa, ciwon sankarau da kwalara”.
Da yake jaddada cewa halin da ake ciki, ya ce duk da cewa babu allurar rigakafin cutar zazzaɓin Lassa, ya jaddada cewa za a iya guje wa cutar zazzaɓin, don haka akwai buƙatar jama’a su ɗauki kiyaye rayuwarsu ta yau da kullum.
A cewarsa, Cibiyar Kula da Cututtuka ta Nijeriya NCDC, Majalisar ɗinkin Duniya da sauran masu ruwa da tsaki na ƙoƙarin ƙaddamar da rigakafin cutar zazzaɓin Lassa.
“Wannan wani muhimmin mataki ne a ƙoƙarin da ake na zaɓurar da ‘yan Nijeriya domin ɗaukar matakan da suka dace don yaƙar waɗannan cututtuka masu saurin kisa musamman a halin yanzu da muke cikin na zafi, lokacin da ake fama da matsalar cutar zazzaɓin Lassa, cutar sanƙarau da kuma kwalara”.
Mallam Issa-Onilu ya ƙara da cewa, “Kamar yadda ku ka sani, zazzaɓin Lassa ya yi sanadin salwantar rayuka a wasu sassan ƙasar nan. An samu ɓullar cutar a garin Saki a shekarar da ta gabata, amma gwamnatin jihar Oyo cikin gaggawa ta zauki matakin daƙile yaɗuwar cutar.”
Ya ƙara da cewa, an wayar da kan jama’a ne domin hana cututuka shiga jihar ta Oyo, don haka akwai buƙatar a canja tsari domin shawo kan yazuwar cututtukan da ake fama da su a lokacin zafi, kamar zazzaɓin Lassa, ciwon sanƙarau da kwalara daga shigowa jihar Oyo.
Da take jaddada muhimmancin tsaftar jiki da muhalli wajen hana yaɗuwar cututtuka, NOA ta ce cin cikakken abinci, ‘ya’yan itatuwa da kuma motsa jiki na hana yazuwar waɗannan cututtuka.
Daraktan NOA na jihar Oyo, Dr. Olukemi Afolayan, yayin da yake magana ya bayyana cewa a halin yanzu hukumar ta fara wayar da kan jama’a game da cutar sanƙarau, kwalara, kyanda, yana mai cewa, “Lafiya ita ce uwar jiki. Don haka, mun yi ta yawo a makarantun firamare da sakandare, domin wayar da kan yaran mu.
“Zazzaɓin Lassa ba ya zama ruwan dare a jihar Oyo, amma a shekarar da ta gabata an samu ɓullar cutar a Saki. Cutar zazzaɓin Lassa na faruwa ne sakamakon kwayar cutar da aka samu a cikin wani nau’in ɓera.”
