Daga DAUDA USMAN a Legas
A ranar Lahadin da ta gabata ne makarantar Madarasatul Tarbiyyatul Islamiyya Wa Ta’alim dake unguwar Rafin Sarkin Zango Bakori a cikin jihar Katsina ta yaye ɗalibai maza da mata 4; maza goma sha biyar, mata talatin da biyu.
Taron ya samu halartar manyan malamai da shuwagabannin makarantun Islamiyoyi na garin Bakori da kewayenta da sauran al’ummar Musulmi bakiɗaya.
Sheikh Kalifan Marigayi Sheikh Alhaji Malam Sa’idu Alti Funtuwa shine ya jagoranci sauran malamai a wajen taron walimar karatun yaye ɗaliban, babban baƙo a wajen taron Alhaji Bello Idris Marigayi Makaman Katsina hakimin Bakori.
Haka kuma taron ya gudana ne a harabar makarantar dake unguwar Rafin Sarkin Zango Bakori a jihar Katsina.
Tun da farkon buɗe taro da addu’a aka ba waɗansu daga cikin malaman da suka samu halartar taron dama suka cigaba da karanto ayoyin Alkur’ani mai tsarki gwargwadon abinda ya sauwaƙa sannan kuma aka sake ba waɗansu daga cikin malaman dama suka cigaba da wa’azantar da al’umma bisa kan muhimmacin sanya yara ƙananu makarantun islamiyoyi domin su koyo karatun Alkur’ani mai tsarki tare da bayyanawa al’ummar Musulmi abubuwan da suka shafi rayuwarsu a nan duniya da ma lahira baki ɗaya.
Hakazalika malaman suka cigaba da wa’azantar da al’ummar Musulmi dangane da watan azumin Ramadan dake shirin kankama anan da ‘yan kwanaki kaɗan masu zuwa.
Bayan malaman sun kammala ne suma yara ɗaliban da makarantar ta yaye aka basu dama ɗaya bayan ɗaya suka cigaba da karanto ayoyin Alkur’ani mai tsarki tare da ingantattun hadisai baki gwargwadon abinda ya sauwaƙa sannan makarantar ta ba ma yara ɗaliban da ta yaye waɗanda suka fi kowa ƙwarewa a fannin karatu kyaututtukan Alƙur’ani mai tsarki domin cigaba da karantawa a kowanne lokaci.
Daraktan makarantar Alhaji Malam Surajo Bello Bakori ya yi jawabin godiya ga dukkan al’ummar da suka zo taya shi murnar gabatar da wannan taro tare da nuna gamsuwarsa ga malaman da suke koyar da ɗaliban makarantar tasa karatu kuma suna fahimta a wajen karanto ayoyin Alkur’ani mai tsarki kamar yadda ya kamata.
Sannan ya cigaba da yin kira ga al’ummar ƙaramar hukumar Bakori cewar ƙofar makarantar a buɗe take haka zalika makarantar madarasatul ulul albab wadda akafi saninta da suna makarantar Malama Zaharau Rafin Sarkin Zango Bakori ta gudanar da nata taron walimar yaye ɗaliban guda goma sha shida maza da mata, inda taron ya samu halartar malamai da iyayen yara da sauran al’umma Bakori bakiɗaya.
Shugabar makarantar Malama Zaharau Rafin Sarkin Zango Bakori ta yi jawabin godiya ga iyayen yara da sauran al’umma baki ɗaya dangane da wannan al’amari.
