Buratai ya yi kira da a kafa rundunar haɗin gwiwa ta tsaro a makarantun ƙasar nan

Spread the love

Daga Sanusi Muhammad, a Gusau 

Tsohon Babban Hafsan Sojin Nijeriya, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kafa rundunar kiyaye makarantu ta haɗin gwiwa a ƙasar nan domin bunƙasa ilimi. 

Laftanar Janar Buratai ya yi wannan kiran ne a jawabin da ya gabatar a taron ƙasa da ƙasa na shekarar 2025 wanda tsangayar ilimi ta Jami’ar Tarayya ta Gusau Jihar Zamfara ta shirya a Jami’ar Tarayya ta Gusau ranar Talata. 

Laftanar Janar Buratai wanda ya samu wakilcin Birgediya Janar MK Galadanchi Mai ritaya a wajen taron ya bayyana cewa, ya kamata rundunar tsaron makarantar ta haɗa da sojoji da ‘yan sanda da shugabannin al’umma. 

“Ta hanyar kafa rundunar tsaro a makarantu na iya samar da ingantattun hanyoyin tsaro ga wuraren da ke da hatsari,” ya ce. 

Ya kuma ba da shawarar cewa amfani da fasahar zamani na sanya ido da suka hada da jirage marasa matuki na iya taimakawa wajen sa ido kan yankunan makarantu masu rauni da kuma dakile hare-haren ta’addanci. 

“Ilimi shine tushen haƙƙin ɗan adam kuma babban jigon ci gaban ƙasa, idan muka gaza kare shi, zamu jefa makomar al’ummarmu cikin haɗari,” inji shi.

“Duk da haka, idan muka tashi kan wannan ƙalubale ta hanyar kirkire-kirkire, haɗin gwiwa da jajircewa ba tare da ɓata lokaci ba, za mu iya tabbatar da cewa kowane ɗan Nijeriya yana da damar samun ingantaccen ilimi,”  Laftanar Janar Buratai ya ɗauka aiki.

Laftanar Janar Buratai wanda ya koka da cewa binciken da hukumar UNICEF ta gudanar a shekarar 2024, ya nuna cewa ‘yan mata na da kashi 60 cikin 100 na yara miliyan 10 da ba sa zuwa makaranta, wadanda galibin su rashin tsaro ya shafa, ya bayyana cewa dole ne a mai da hankali ga yara masu nakasa waɗanda ke fuskantar ƙalubale wajen samun ilimi. 

By ukarofi