
Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta gargaɗi Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara da ya daina ruɗar da al’umma akan sauya sheƙa da ƴan siyasa suke yi musamman ƴan majalisar dokoki.
Babban Sakataren yaɗa labarai na Shugaban hukumar, Rotimi Oyekanmi ya bayyana hakan a wata takarda a ranar Juma’a, inda ya gargaɗi gwamnan akan ɗora wa INEC alhakin ɗaukar ɓangare wajen maye guraben da aka samu daga masu sauya sheƙa a ƴan majalisun dokoki na jihohi da na ƙasa.
Ya ce, babu wata hujja da gwamnan ya bayar wajen kare zargin nasa akan hukumar.
Fubara ya zargi INEC ne da ƙin cike guraben da aka samu a sanadin rikicin siyasar majalisar dokokin jiharsa ta Ribas, inda aka samu ɓangarori biyu na ikirarin shugabanci.
Saidai Oyekanmi yi ya bayyana cewa, waɗannan matsaloli na rikicin siyasa a Ribas da ma wasu duk suna kotuna ciki har da waɗanda ke Kotun Ƙoli, kuma suna jiran hukunci.
Ya kuma yi kira ga mutane masu riƙe da madadin iko da su kiyaye kalaman da za su riƙa bayyana wa al’umma don kada su ruɗar da su musamman game da batutuwan da ke kotuna.
