
Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya yi tsokaci game da batun zargin cin zarafi da Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi akan Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio.
A wata sanarwa da Saraki ya fitar a ranar Asabar, ya koka kan rikicin inda ya ce hakan abu ne da ka iya rage darajar majalisar matuƙar ba a tabbatar da gaskiya da adalci wajen yin hukunci ba a matsayinta na mafi girman reshen gwamnati.
Ya shawarci ɓangarorin biyun da magoya bayansu da su kiyayi ƙalubalen da kalamansu ka iya haifarwa, inda ya yi kira a gare su da su fifita darajar majalisar akan ra’ayoyinsu na kai-da-kai.
Saraki ya kuma yi kira da a tabbatar da bin ƙa’idojin doka da nuna ƙwarewa a yayin warware rikicin, ya na mai kira ga kwamitin kula da sanin makamar aiki da ƙararraki da ya yi adalci a yayin hukunci kan batun.
Haka kuma, Saraki ya yi kira ga Akpabio da Akpoti da su bai wa kwamitin haɗin kai don tabbatar da adalci a yayin hukuncin.
Har’ilayau, Saraki ya yi gargaɗin kada a bar majalisar ta zama fagen da ke sakaci game da batutuwan rashin ladabi da suka ƙunshi cin zarafi da tauye jinsi da cin mutuncin aiki da abubuwa makamantansu.
