
Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon mai taimaka wa tsohon Shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, Dakta Doyin Okupe ya rasu.
A safiyar ranar Juma’a ne Dakta Okupe, mai shekaru 72 ya rasu, bayan fama da wani gajeren rashin lafiya da ake kyautata zaton cutar daji ce.
A shekarar 2022 ne aka naɗa shi a matsayin Darakta-Janar na jam’iyyar LP na zaɓen Shugaban ƙasa na 2023.
Daga bisani aka tilasta masa yin murabus sakamakon zarginsa da badaƙalar wasu kuɗaɗe.
