Kotu ta dakatar da Majalisar Dattawa daga ɗaukar matakin ladabtarwa kan Natasha

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da kwamitin Majalisar Dattawa mai Kula da Ladaftarwa da ɗa’a daga ɗaukar matakin ladabtara a kan Natasha Akpoti-Uduaghan.

Mai shari’a Obiora Egwuatu, ya bayar da umarnin ne a ranar Talata bayan wata takardar da lauyoyin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan (mai wakiltar Kogi ta tsakiya) suka gabatar.

An gayyaci Akpoti-Uduaghan da ta bayyana a gaban kwamitin ladabtarwa na majalisar dattijai bayan wata hatsaniya da shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio a ranar 20 ga watan Fabrairu.

Idan za a iya tunawa, Sanata Akpoti-Uduaghan ta kawo cikas ga zaman majalisar ta hanyar ƙin amincewa da kujerar da aka ba ta, inda ta bijire wa umarnin Akpabio da kuma tada wani batu a kai a kai duk da cewa an yi watsi da su.

Daga bisani, majalisar dattijai ta miƙa Akpoti-Uduaghan ga kwamitin ɗa’a don duba matakin ladabtarwa.

A ranar 28 ga Fabrairu, a wata hira da aka yi da ita a gidan talabijin na Arise, Sanatan na Kogi ta yi zargin cewa rikicinta a majalisar ya fara ne bayan ta ƙi amincewa da buƙatar lalata da shugaban majalisar dattawan.

By ukarofi