Kocin Super Eagles ya ajiye Ahmad Musa, ya zuba ƴan wasan gida a jerin ƙarshe na wasannin neman gurbi a Kofin Duniya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Kocin Super Eagles, Éric Sekou Chelle, ya soke sunan Kyaftin ɗin tawagar, wato Ahmad Musa a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda za su fafata a wasannin neman gurbin shiga gasar Kofin Duniya na 2026.

Super Eagles za ta buga wasanni biyu ne da ƙasashen Ruwanda da Zimbabwe a watan Maris.

A ranar 21 ga wata ne ƙungiyar za ta fafata da takwararta ta ƙasar Ruwanda, bayan kwanaki huɗu kuma za ta buga da Zimbabwe a Filin wasa na Godswill Akpabio dake Uyo a Jihar Akwa-Ibom.

Ga tawagar ƴan wasa 23 da kocin ya zaɓo a jerin ƙarshe da za su buga wasanni biyun kamar yadda Blueprint ta ruwaito:

“Goalkeepers: Stanley Nwabali (Chippa United, South Africa); Amas Obasogie (Singida Blackstars, Tanzania); Kayode Bankole (Remo Stars).”

Sai kuma ƴan wasan baya da suka haɗa da “William Ekong (Al-Kholood FC, Saudi Arabia); Bright Osayi-Samuel (Fenerbahce SK, Turkey); Bruno Onyemaechi (Olympiacos FC, Greece); Calvin Bassey (Fulham FC, England); Olaoluwa Aina (Nottingham Forest, England); Igoh Ogbu (SK Slavia Prague, Czech Republic).”

Sauran sun haɗa da “Midfielders: Wilfred Ndidi (Leicester City, England); Raphael Onyedika (Club Brugge, Belgium); Alhassan Yusuf Abdullahi (New England Revolution, USA); Alex Iwobi (Fulham FC, England); Joseph Ayodele-Aribo (Southampton FC, England); Papa Daniel Mustapha (Niger Tornadoes).”

“Forwards: Samuel Chukwueze (AC Milan, Italy); Victor Osimhen (Galatasaray FC, Turkey); Ademola Lookman (Atalanta FC, Italy); Victor Boniface (Bayer Leverkusen, Germany); Simon Moses (FC Nantes, France); Sadiq Umar (Valencia FC, Spain); Nathan Tella (Bayer Leverkusen, Germany); Tolu Arokodare (KRC Genk, Belgium)”, kamar yadda Blueprint ta ruwaito.

By Babaji