Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) ta karrama kwamishinan kimiyya, fasaha da ƙirkire-ƙirkire na jihar Kano, Dr. Yusuf Kofar Mata, da kwamishinan bayanai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, da lambar yabo ta jakadancin yaƙi da miyagun ƙwayoyi.
An ba su wannan karramawa ne saboda jajircewarsu wajen yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi da kuma ƙoƙarin farfaɗo da matasa daga ɗabi’un miyagun ƙwayoyi.
Kwamitin farfaɗo da zaman lafiya da gyaran halayen matasa na jihar Kano ƙarƙashin shugabancin Dr. Yusuf Kofar Mata ya kai ziyara ga manyan masu ruwa da tsaki, ciki har da kwamandan NDLEA na jihar Kano da kwamitin malamai (Council of Ulamas) don neman haɗin kai.
A ziyarar da suka kai fadarsa, Sarkin Kano, Alhaji Sunusi, ya yabawa kwamitin kan wannan ƙoƙarin, tare da alƙawarin cikakken goyon bayan masarautar wajen cimma nasara.
Haka kuma, kwamitin ya buƙaci malaman addini su yi amfani da tafsirin azumi da huɗubobin Juma’a don wayar da kan iyaye da sauran al’umma kan muhimmancin kare matasa daga ɗabi’un miyagun ƙwayoyi da munanan halaye.
