
Daga BELLO A. BABAJI
Sanatar da aka dakatar daga Majalisar Dattawan Nijeriya, Natasha Akpoti-Uduaghan, wadda ke wakiltar Jihar Kogi ta Tsakiya, ta kai batun rikicinta da Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio zuwa mataki na duniya.
Ta yi hakan ne a yayin zaman majalisar dokoki ta Majalisar Ɗinkin Duniya da ke bai wa mata daman gabatar da batutuwansu, wanda aka gudanar a birnin New York.
Ta ce, tana neman a yi mata adalci ta hanyar shigo da cibiyoyin demokraɗiyya a mataki na duniya cikin batun.
Ta kuma bayyana dakatar da ita daga Majalisar Dattawan a matsayin abinda aka yi ba bisa doka ba.
An dai dakatar da Natasha ne bayan samun tsama da ta yi da Akpabio akan batun sabon tsarin zama a majalisar, wanda ta ce ya sa ta yanayi na takura.
Hakan ya biyo bayan ƙin karɓar gudunmawarta ne da Shugaban majalisar ya yi, saboda ba ta bi umarnin yin magana daga kujerar da aka ware mata ba a majalisar.
Lamarin ya yi ƙamari ne a lokacin da aka ga Natasha a gidan telebijin na ƙasa tana ɗora zargin cin zarafin da Akpabio ya yi mata a matsayin dalilin hukunta ta sakamakon ƙin amincewa da buƙatarsa da ta yi.
Haka kuma, ta shigar da takardar ƙorafi a majalisar, inda ta bayyana yadda Akpabio ya yi ƙoƙarin cin zarafin nata.
