Labarin littafin ‘A Gentle Breeze” ya sa ni kuka ya sa ni dariya – Kabiru Musa Jammaje

Spread the love

DAGA MUKHTAR YAKUBU

 Idan ana magana a game da marubuta da suka bayar da gudunmawa a ƙasar Hausa musamman ta fuskar matasa, to Malam Kabiru Musa Jammaje yana cikin sahun gaba. 

Duk da kasancewar sa marubucin harshen Turanci ne shi, amma gudunmawar da ya bayar ta zarta ta wasu marubutan Harshen Hausa ne ba kusa ba. Domin kuwa kasancewar sa malami a harshen Turanci, ta sa ya rinƙa buga littattafai domin koyon harshen Turanci a tsakanin matasan mu, wanda hakan ya sa matasa da dama suka koyi yaren Turanci cikin sauƙi kuma har suka zama abin alfahari a gare mu.

Duk da littattafan da ya rubuta na koyon harshen Turanci ne, a yanzu Malam Kabiru Musa Jammaje ya fitar da wani sabon littafin na sa ƙirƙirarren labari mai suna ‘A Gentle Breeze’, wanda ya bayyana a kasuwa tun a ranar 26 ga Disamban da ya gabata 2024 kuma aka fara sayar da shi a taron bikin ranar Jammaje ta ƙarshen shekara.

Ganin yadda marubuci Kabiru Musa Jammaje ya sauya salon rubutun sa daga koyar da harshen Turanci zuwa rubutun ƙirƙirarren labari ne ya sa wakilinmu ya tattauna da shi, don haka sai ku biyo, ku ji yadda tattaunawar ta kasance.

MANHAJA: Malam Kabiru Musa Jammaje kai marubuci ne na koyar da yaren Turanci da ƙa’idojin sa, amma dai a wannan lokacin ka fara fitar da littafi na ƙirƙirarren labari, kamar yadda muka gani a sabon littafin ka mai suna ‘A Gentle Breeze’. Masu karatun mu za su so su ji ƙarin bayani daga gare ka.

JAMMAJE: To gaskiya ne, na kwashe tsawon lokaci ina rubuce-rubuce na littattafai, da suka shafi koyon harshen Turanci da kuma ƙa’idojin sa a matsayina na malamin Turanci, kuma shugaban makarantar da take koyar da Turanci a duk faɗin ƙasar nan, wato Jammaje Academy. To sai ya zama littattafai da nake yi sun shafi koyar da Turanci da kuma magance kura-kuran da ake yi wajen yin Turancin kamar nahawu da kalmomi da sauran su, a taƙaice dai littattafai da za su gyara Turanci da kuma yadda za a inganta shi. Ko da yake na yi wani mai suna ‘General Knowledge’, da kuma wani da na yi da na fito da labarai na tafiye-tafiye da na yi. Kuma ina ganin daga kansa ne na yi tunanin abin ya yi tasiri a gare ni, na tunanin fara rubutun ƙirƙirarren labari. Kuma Alhamdulillah a yanzu ga shi ‘A Gentle Breeze’ ya fito, wanda ya kasance shi ne ƙirƙirarren labari na farko  kenan da na fitar wanda kuma zan ci gaba da yin wasu nan gaba.

Shi wannan littafin mai ya ƙunsa?

To labarin dai na wani farfesa ne da zai aurar da ‘yar sa guda ɗaya wadda ta kasance kyakkyawar mace wadda na saka mata suna Sulaiha. Ta kasance iyayen ta suna son ta yi aure, kuma ta kasance mai samarin da suke neman auren ta da yawa. To a cikin maneman auren nata sai ta fito da mutane sha biyu da nufin cewa mahaifinta ya zaɓi mutum ɗaya a ciki. Saboda haka sai ya fara ganawa da su ɗaya bayan ɗaya duk wanda aka gama sai ya fita wani ma ya shigo.

Sai dai kuma duk wanda ya zo ganawar sai ya bada labari, saboda ita Zulaiha tana son bada labari, don haka duk wanda ya shigo ya gabatar da kansa da karatun da ya yi, to kuma sai ya bada labari mai daɗi. To irin wannan labaran ne aka harhaɗa ya tayar da labarin  ‘A Gentle Breeze’. 

Shi rubutu ya kan yi tasiri  ba ga masu karanta su kaɗai ba har ma da wanda ya rubuta. Wanne irin tasiri rubutun wannan littafin ya yi a gare ka?

To gaskiya ka ga idan har mutum ya karanta ‘A Gentle Breeze’ zai yi tasiri a gare shi, saboda ni ma ya yi mini tasiri, don akwai wasu abubuwa na ilimi da yawa da aka saka musamman abin da ya shafi tarihi. Sannan akwai abubuwa na nishaɗi, don ko ni da na rubuta, wasu labaran da suke ciki suna saka ni dariya . 

Sannan da akwai wani jarumi da na saka a ciki shi kuma ya saka ni kuka , don haka ni ma labaran sun yi mini tasiri sosai, kuma ina ganin za su yi wa masu karatu tasiri.

To an san littafin ka duk a makarantar ka kake sayarwa ga ɗaliban ka, ko shi ma ‘A Gentle Breeze’ sai a makarantar ka za ka sayar da shi?

To shi wannan littafin kowa zai iya saya, don ina son ya shiga ko’ina ba sai ɗalibai na ba kaɗai. Kuma gaskiya ne littattafai da nake rubutawa an fi samun su a wajen ɗalibai na da makarantun da muka kafa. Amma shi wannan zai shiga hannun kowa ba sai ɗalibai na ba kaɗai, tun da ka ga shi ba darasi ba ne. Shi wancan na darasi ne da ake koyar da ɗalibai a aji, wannan kuma labarai ne a ciki wanda ake son kowa ya karanta, kuma a haka ne zai shiga ko’ina duk inda kasuwa take  za a kai shi domin masu buƙata su same shi cikin sauƙi.

Kamar aƙalla littattafai da ka rubuta za su kai guda nawa?

To gaskiya suna da ɗan yawa sun kai guda 20 ko sama da haka. Kamar daga cikin su akwai;

‘A New way of Learing English’, ‘Dependable English’, ‘A Practical Way of Speaking English’, ‘English for Beginners’, ‘Basic Literature’, ‘British Stories’, ‘Better Pronunciation English for All’, ‘The 1000 Words ɓia Freedom Radio’, ‘Wrong English versus Right English’, ‘Crossing Borders’, ‘Basic World History’, ‘2000 Sentences and Their Meanings’, ‘Business English’, ‘Teach Yourself British English’, ‘Words and Proverbs’, ‘Beautiful English’, ‘English for Students’, ‘General Knowledge for  Nigerian Schools’, ‘Another way of Leaning English’, ‘Leaning to Read and Write  Easily’, ‘Everyday English Conyersations’, ‘A  Gentle Breeze’.

To daga ƙarshe, wanne saƙo ka ke da shi ga masu karatu?

To ɗan abin da zan ƙara da shi shi ne, shi dai ‘A Gentle Breeze’ ba wani ƙaton littafi ba ne, shafi 100 ne kawai. Tun da yanzu mutane suna da ayyuka, don haka ni ban yi imani na yi ƙaton littafi ba, na fi so na yi wanda mutum zai karanta shi lokaci guda ya ɗauki darasin da yake ciki, don haka zama ɗaya ko biyu mutum zai iya karancewa. Fatan mu dai kowa ya yi amfani da darasin da yake ciki. Ina fatan littafin zai amfanar da jama’a.

To madalla mun gode.

Ni ma nagode sosai tare da fatan alheri.

By ukarofi