Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Mata da suka rasa mazajen su da masu ƙaramin ƙarfi suka amfana da shinkafa mai nauyi 25kg da kuɗi Naira 10,000 kowanne su.
Gwamna Dikko Raɗɗa ya ƙaddamar da bada tallafin a gidan Gwamnatin jihar inda ya fara rabawa mata 840 da suka fito daga ƙananan hukumomin Katsina,kaita, Rimi da Ɓatagarawa.
A jawabinsa malam Dikko Raɗɗa ya bayyana shirin a matsayin ɗaya daga cikin ƙudurin gwamnatin sa na inganta rayuwar al’ummar jihar musamman masu ƙaramin ƙarfi.
Ya ce wannan tallafi da aka ba waɗannan zawarawa anyi shine domin dawo masu da marataba da damar da suke da ita na inganta rayuwar su da suma za su bada tasu gudummawa ga tattalin arzikin jihar.
Gwamna Raɗɗa ya kuma yaba da irin gudunmawar da ma’aikatar kula da addinin musulunci da sauran masu ruwa da tsaki suka bada wajen tabbatar da wannan shiri.
Yayi kira ga waɗanda suka amfana da tallafin,da suyi amfani da shi wajen kyautata wa iyalan su maimakon su kai kasuwa su sayar.
Gwamnati na kowa da kowa ne, babu wanda za a barshi a baya, domin haka kowa ya zo ya bada tashi gudummawa wajen ciyar da jihar gaba”inji Dikko.
Tunda farko, kwamishinan ma’aikatan harkokin addinin Muslunci Hon Ishaq Shehu Dabai ya bayyana cewa matan da suka fito daga ƙananan hukumomi 34 da ke jihar suka amfana da tallafin.
