Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ya zuwa yanzu kujeru 3,680 da hukumar alhazzai ta ƙasa ta ware wa jihar Katsina, mutane 1,850 kaɗai suka biya kuɗin kujerar.
Daraktan hukumar alhazzai na jihar Alhaji Yunus Abdullahi Dankama ya sanar da haka a taron hukumar gudanarwa na hukumar a Katsina.
Ya shaida masu Kamfanin jiragen sama na Max Air hukumar alhazzai ta ƙasa ta amincewa jihar da zai kwashe maniyatan bana.
Daraktan ya ƙara da cewa Jihar Katsina tace za ta zama ta ƙarshe wajen kwasar maniyatan ta zuwa ƙasa mai tsarki kamar yadda hukumar alhazzai ta ƙasa ta tsara.
Ya yaba wa Gwamna Dikko Raɗɗa kan kulawa da goyon baya da yake bai wa hukumar wajen gudanar da harkokin ta na yau da kullum.
