Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
An yi kira ga al’ummar ƙaramar hukumar Bebeji akan su haɗa kai ba tare da nuna bambancin siyasa ba, su zaɓo mutane maso son kishin yankin domin tura su majalisar dokoki ta jihar Kano domin su wakilce su a zabe mai zuwa domin ceto yankin daga halin da take ciki na koma baya.
Wani ɗan asalin yankin Abba Umar Tiga ne yayi kiran da yake zantawa da yan jarida ya ce al’ummar ƙaramar hukumar Bebeji basa samun wani kyakkyawan tagomashi na cin gajiyar romon damakwaradiyya daga wakilai da suke turawa majalisar jihar Kano tun daga dawowar tsarin damakwaradiyya 1999.
Malam Abba Umar Tiga da shima ɗan gwagwarmayar siyasa ne ya ce yanzu babu wani waje da zaka shiga a sassan yankin ka sami wani muhimmin aiki da za ayi tutiyar wani ɗan majalisa na jiha ne ya kawo tsakanin na da da na yanzu.
Ya yi nuni da cewa hatta tsohon ɗan majalisar jiha na Bebeji da na yanzu ya gada ya yi wakilci shekara 12 shi ne ma ya fi kowa cin moriyar zuwa majalisa sau uku a jere ,amma babu wani aiki da zaka nuna da za ayi alfahari ya kawo a yankin har ya gama.
Sannan shi kuma na yanzu da ya kuma daya gaje shi sammakal domin cikin shekara biyu ba wani abu na azo a gani da ya ke hatta ma garin ya daina zuwa gara na baya a lokacinsa yana ɗan leƙowa.
Ya ƙara da cewa yanzu haka ruwan sha na ɗaya daga cikin manyan matsaloli da ya fi ciwa al’ummar yankin tuwo a kwarya duk da suna da babban Dam amma yanzu ta kai jarkar ruwa ya kai N100 ga koma baya da ake dashi a harkar ilimi da fannin lafiya da bai wani motsi da ake ji na kawo ɗauki da ɗan majalisar su na jiha yake.
Abba Umar Tiga ya ce akwai mutane masu kishi da son cigaban jama’a da zasu zama masu faɗa da cikawa a Bebeji a ya zama wajibi al’ummar yankin a ajiye batun bambancin siyasa a duba dacewa da kishi da cancanta a tasa shi a gaba hakan zai sa a sami sauyi da al’umma zasu amfana.
Sai dai kan wannan iƙirarin mun yi ƙoƙarin ji ta bakin ɗan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar ƙaramar hukumar Bebeji, Hon. Ali Tiga har zuwa rubuta labarin ba mu samu jin ta bakinsa ba.
