Mene ne yake kawo magwas da matakan kiyayewa lokacin azumi?

Spread the love

Tare da CHIROMA AMINU ASID

Mene ne magwas (acid reflux or eguitation)?

Magwas yana nufin yawan gyatsa da jin abinci yana hawa daga ciki zuwa maƙogwaro, wanda ke sa rashin jin daɗi, wanda kuma yake yawan faruwa, musamman bayan an yi sahur da safe.

Hakan na faruwa ne, saboda sinadarin ‘acid reflux’, wato lokacin da ruwan ‘acid’ na ciki ya tashi ya yi sama.

Haka nan kuma, magwas yana nufin yawan gyatsa da jin abinci yana hawa daga ciki zuwa makogwaro, wanda ke sa rashin jin daɗi musamman bayan sahur. Hakan na faruwa ne saboda acid refluɗ, wato lokacin da ruwan acid na ciki ya tashi sama.

Abubuwan da suke haddasa magwas lokacin azumi:

-Cin abinci mai yawa sosai a lokacin yin sahur.

-Idan ciki ya cika fiye da kima, yana matsa wa murhun narkewar abinci (sphincter), yana sa acid da abinci su taso sama.

-Cin abinci mai yawan kitse da mai.

-Abinci kamar nama mai kitse, miyar manja, kosai, ‘chips’ da soyayyen abinci suna da wahalar narkewa, suna jawo gyatsa da nauyin ciki.

-Shan ruwa mai yawa da wuri.

-Idan aka sha ruwa da yawa lokaci guda bayan cin abinci sannan a koma bacci yana iya cika ciki da wuce kima, yana haddasa gyatsa ko abun sha masu ruwa kamar kunu idan aka sha su da yawa sannan aka koma bacci Nan take bayan sahur.

-Shan abin sha mai gas (‘soft drinks, flaɓored drinks’).

-Shan ‘Coke, Fanta, Sprite, Tiara’ da ‘Jolly Juice’ na ƙara hayaƙin gas a ciki, yana haddasa gyatsa da magwas.

-Kwanciya nan take bayan sahur.

-Idan mutum ya kwanta bayan sahur, ‘acid’ daga ciki zai tashi zuwa saman baki, yana haddasa gyatsa da jin kuna a ƙirji (‘heartburn’).

-Cin abinci mai yawan ‘sugar’ da ‘carbohydrates’.

-Taliya, shinkafa da kayan ƙwalama suna sa suga ya tashi da sauri sannan ya sauka cikin lokaci ƙalilan, yana haddasa kasala da gyatsa.

-Shan madara mai nauyi.

-Madara mai yawa tana rage kuzari kuma tana iya jawo gyatsa da jin nauyin ciki.

Masha Allah. A sha ruwa lafiya.

By ukarofi