Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban ƙungiyar kwamred Mannir Suleiman ya faɗi haka a lokacin da ya’yan ƙungiyar su ka kawo wa shugaban ƙaramar hukumar Funtua mai barin gado Hon Sani lawal ziyarar ban girma a ofishin sa.
Kwamred Mannir Suleiman ya bayyana cewa abinda ƙungiyar ta sa a gaba shine tabbatar da samar da ingantaccen ilimi,kiwon lafiya da taimakawa marasa ƙarfi da neman dama ta ayyuka a hukumomin gwamnati.
Ya ce sun kawo masa ziyara ne domin kulla alaƙa ta ‘yan uwantaka a ƙaramar hukumar.
Ya kuma bayyana shugaban ƙaramar hukumar a matsayin haziƙin mutum mai gaskiya da riƙon amana da za a daɗe ana kewar sa .
” Koda yaushe Kofar sa a buɗe ta ke a duk lokacin da al’ummar sa ke buƙatar ganin sa domin cigaban ƙaramar hukumar”inji kwamred Suleiman.
A jawabinsa, shugaban ƙaramar hukumar Hon Sani lawal ya nuna jin daɗin sa bisa wannan ziyarar da irin wannan ƙungiya mai daraja ta yi masa a dai dai lokacin da yake shirin barin ofishin.
Sai yayi kira a gare su da su zage damtse wajen tunkarar ƙalubale na samar da kyakkyawar cigaba a yankin Funtua da jiha baki ɗaya.
Ya kuma yi kira ga sauran ƙungiyoyi da su haɗa hannu da wannan ƙungiya domin cimma nasarar tafiyar.
Hon Sani lawal ya yi alƙawarin bada tasa gudummawar wajen samar da cigaba ga wannan ƙungiya tare da tabbatar da yankin Funtua ya ƙara kai wani mataki na cigaba.
