
Daga BELLO A. BABAJI
Jamhuriyar Nijar na neman agajin Nijeriya sakamakon ƙarancin man fetur da ta ke fama da shi duk cewa akwai tsamin dangantaka na tsawon watanni a tsakanin ƙasashen biyu.
Rahotanni sun bayyana cewa, wasu manyan jami’an gwamnatin mulkin soji na Nijar sun je Abuja domin ganawa da wakilan Shugaba Tinubu.
Bayan tattaunawar ne aka amince da kai wa Nijar tankokin fetur guda 300.
Wani babban jami’in gwamnati ya ce, Nijeriya ta amince wa buƙatar takwararta ne don hakan ya zama ɗaya daga cikin jinshiƙan sulhu a tattaunawar da suke yi a tsakanin su.
Ya ce, tawagar jami’an na Nijar sun shaida masu cewa ƙasar ta dogara ne da samun fetur daga wata matatar mai a Chana, wadda daga baya aka samu matsalolin da suka sanya aka rufe ta, lamarin da ya sanya ta a halin ƙarancin fetur.
Ya kuma ce, ya na ganin akwai yiwuwar ƙasar ta koma cikin ƙungiyar ECOWAS kasancewar ba ta da wadataccen arziƙin da zai samar wa ƴaƴanta abinci isasshe.
Hakan ya biyo bayan matsanancin ƙarancin fetur ne da Nijar ke fama da shi , wanda ya kai ga sayen litar fetur akan N8,000 a wasu sassan ƙasar, makon da ya gabata.
